ASUU ta yi kaca-kaca da Buhari, Minista, ta ce ta shafe watanni 7 babu albashi

ASUU ta yi kaca-kaca da Buhari, Minista, ta ce ta shafe watanni 7 babu albashi

- Kungiyar ASUU ta bayyana cewa ba ta da shirin dawowa bakin aiki nan kusa

- Ade Adejumo ya musanya maganar da Gwamnatin Tarayya ta yi kwanan nan

- Farfesan ya bayyana abin da ya sa su ke yajin-aiki da kuma abin da su ke nema

A ranar Laraba, 30 ga watan Satumba, kungiyar ASUU ta malaman Jami’an Najeriya ta yi magana game da yajin-aikin da ta dauki tsawon lokaci ta na yi.

ASUU ta bayyana cewa ba ta da shirin janye yajin-aiki har sai gwamnati ta biya ta bashin albashin watanni uku zuwa bakwai da malaman jami’a su ke bi.

Bayan haka, ASUU ta ce dole a amince da manhajar UTAS da su ka kawo domin a rika biyan albashin malaman jami’o’i, idan ana so a bude makarantu.

KU KARANTA: Babu yajin aiki, Kungiyar kwadago ta cin ma matsaya da Gwamnati

Jaridar Business Day ta rahoto Farfesa Ade Adejumo, wanda shi ne shugaban kungiyar ASUU na reshen Ibadan, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar.

Kungiyar malaman ta karyata Ministan kwadago, Chris Ngige, na cewa yajin-aikin da ake yi ya kusa zuwa karshe, Farfesa Ade Adejumo ya ce ko kusa.

Farfesan ya ce gwamnati ba ta cika alkawuran da ta yi ba, daga ciki akwai batun alawus, yarjejeniyar 2009, inganta jami’o’i da kuma karin albashi.

Ade Adejumo ya ce abubuwa uku su ka sa ASUU ta tafi yajin-aiki, manufofin gwamnatin tarayya na rashin tausayi, watsi da harkar ilmi da karya alkawari.

KU KARANTA: Yajin aikin da ASUU ta tafi ya saba doka - Gwamnati

ASUU ta yi kaca-kaca da Buhari, Minista, ta ce ta shafe watanni 7 babu albashi
Shugabannin ASUU da Ministan kwadago Hoto: Labor NG
Asali: UGC

Adejumo ya ke cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari mai-ci, ta ba ASUU kunya, domin kuwa sun yi tunanin za ayi yaki da rashin gaskiya a Najeriya.

Jagoran na ASUU ya ce gwamnatin APC ta raina malaman jami’a, sannan ba ta damu da sha’anin ilmi ba. Ya ce sai an biya masu bukatu kafin a bude makarantu.

A makon nan ne Dr Chris Ngige ya ce za su gana da kungiyar malaman ASUU. Ministan kwadagon ya ce dogon yajin-aikin ya kusa zuwa karshe.

Ngige ya kuma bada tabbacin cewa kwanan nan kungiyar ta ASUU za ta janye yajin aikin nata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel