Mu farka: Yan bindiga sun kusa kutsawa Abuja - Dan majalisar tarayya ya koka

Mu farka: Yan bindiga sun kusa kutsawa Abuja - Dan majalisar tarayya ya koka

- Mamba mai wakiltan mazabar Bosso/Paikoro a majalisar wakilai, Shehu Beji, ya koka a kan yadda yan bindiga suka kusa kutsawa babbar birnin tarayya

- Beji ya yi kira ga sauya tsarin rundunar sojin kasar tare da sauya shugabanninsu

- Dan majalisar ya ce idan har ba a dauki matakin gaggawa ba kan lamarin tsaro, Najeriya za ta tsinci kanta a yanayi irin na Rwanda da Somalia

Wani dan majalisar wakilai, Shehu Beji, ya koka a kan yadda yan bindiga suka kusa kutsawa ta shiyar babbar birnin tarayya, Abuja.

Kwanan nan ne dai yan bindiga suka kai hari yankin Tungan Maje da ke Abuja, inda suka yi garkuwa da mutane sannan suka bukaci a biya kudin fansa.

Beji, a zauren majalisa a ranar Laraba, ya gabatar da wani kira mai taken, "kira ga samar da sansanin sojoji don dakile hare-haren yan bindiga a kananan hukumomin Shiroro, Rafi da Munya da ke jihar Neja wanda ke yaduwa zuwa garuruwan Kafinkoro, Ishau da Adunu a karkashin mazabar Bosso/Paikoro."

Beji, a kiran nasa, ya koka kan cewa “ci gaba da barin shugabannin tsaro da aka yi na iya zama tushen matsalar da ake fama dashi, domin dabarunsu ya zama tsohon yayi.”

KU KARANTA KUMA: Tabarbarewar Najeriya: Buhari ya dora laifi a kan Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan

Mu farka: Yan bindiga sun kusa kutsawa Abuja - Dan majalisar tarayya ya koka
Mu farka: Yan bindiga sun kusa kutsawa Abuja - Dan majalisar tarayya ya koka Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

A cewarsa, matsalar rashin tsaro ta kai intaha da idan ba’a magance ta cikin gaggawa ba, Najeriya na iya tsintar kanta a hatsari irin na kasashen Rwanda, Somalia da sauransu.

Ya bayyana cewa mazabar Shiroro/Rafi/Munya na dauke da kananan hukumomi uku, wanda biyu daga cikinsu ke kusa da mazabar Bosso/Paikoro na jihar Niger.

Ya koka a kan hare-haren da ake ta kai wa kananan hukumomin Rafi da Shiroro na jihar Niger, inda ake rasa rayuka da dukiya a kullun, cewa akwai bukatar yin garambawul a tsarin rundunar soji cikin gaggawa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kama mutum 30 yayinda ake zanga-zangar juyin-juya-hali a Lagas

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki.

Ya ce hakan kuwa daidai yake da kowacce kasa domin kuwa dukkan duniya ne ake cikin wannan halin.

Buhari ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga 'yan Najeriya a ranar da kasar ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.n

Source: Legit

Online view pixel