Kotu ta bayar da belin matashi a kan N200,000 bayan an sameshi da lafin yunkurin kashe kansa

Kotu ta bayar da belin matashi a kan N200,000 bayan an sameshi da lafin yunkurin kashe kansa

- Laifine a Najeriya mutum ya yi yunkurin kashe kansa ta kowacce irin hanya

- Wanda aka samu da laifin aikata hakan zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara guda a gidan yari

- Ana yawan samun labarin cewa matasa su na hallaka kansu ko kuma yunkurin aikata hakan sakamakon matsi da kuncin rayuwa

Rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta tsare wani matashi, Solomon Okon, na tsawon wata guda bayan ya yi yunkurin kashe kansa.

Solomon ya sha wani sinadari mai guba da niyyar ya kashe kansa saboda ya rasa aikinsa.

Lamarin ya faru ne a cikin watan Agusta bayan an damkawa Solomon takardar sallamarsa daga aiki a wani asibiti mai zaman kansa.

Wani makusancin Solomon ya bayyana cewa jami'an 'yan sanda sun tsare shi kafin daga bisani su gurfanar da shi a gaban kotu.

"Okon ya na aiki ne a wani asibiti mai zaman kansa kuma N35,000 ne albashinsa a wata.

DUBA WANNAN: Kano: Kotu ta zartar da hukuncin daurin wata 7 a kan mashayin tabar wiwi

"Da wannan albashi ya ke dawainiya da mahaifiyarsa da ke jihar Akwa Ibom, amma sai ya samu takardar sallama daga aiki a watan Agusta.

"Bacin ran an sallame shi daga aiki ne yasa Solomon ya sha sinadari mai guba domin ya mutu, ya bar duniya, amma an samu nasarar ceto rayuwarsa da ya ke a asibiti lamarin ya faru," a cewar makusancin Solomon.

Kotu ta bayar da belin matashi a kan N200,000 bayan an sameshi da lafin yunkurin kashe kansa
Kotu ta bayar da belin matashi a kan N200,000 bayan an sameshi da lafin yunkurin kashe kansa
Source: UGC

Jaridar Punch ta rawaito cewa hukumar asibitin ta damka Solomon a hannun rundunar 'yan sanda.

DUBA WANNAN: Tonon asiri: An gurfanar da Baturen Ilimi da ya sace kudin ciyar da dalibai

Bayan rundunar 'yan sanda ta gurfanar da Solomon ne sai kotu ta amince da bayar da belinsa a kan N200,000.

Sai dai, wani dan uwa wurin Solomon ya ce ba su da kudin belin da kotu ta saka.

Laifi ne mutum ya yi yunkurin kashe kansa a Najeriya, kamar yadda sashe na 327 na kundin manyan laifuka ya bayyana.

Wanda aka samu da laifin aikata hakan zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara guda a gidan yari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel