Banda asarar dukiya: Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 40 a Jigawa

Banda asarar dukiya: Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 40 a Jigawa

- Hukumar SEMA ta jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum 40 da yayinda dubbai suka rasa muhallai da gonakinsu sakamakon iftila’in ambaliyar ruwan

- Lamarin ya afku ne a yankin Hadeja da ke jihar

- Sai dai kuma shugaban hukumar ya ce an kammala duk tsare-tsare don tura kayan tallafi ga mutanen da lamarin ya cika da su

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA), ta tabbatar da cewa akalla mutum 40 ne suka rasa rayukansu yayinda dubbai suka rasa muhallai da gonakinsu sakamakon ambaliyar ruwan da ta cika da yankin a ‘yan kwanakin nan.

Babban sakataren SEMA, Alhaji Sani Ya’u Babura, wanda ya tabbatar da rasa rayukan, ya ce an kammala duk tsare-tsare don tura kayan tallafi ga mutanen da lamarin ya cika da su.

Babura ya ce ana kokarin ganin an samu ainahin alkaluman mutanen da suka rasa muhalli da wadanda suka rasa gonakinsu.

Baya ga haka, ya ce gwamnatin jihar za ta nemi tallafin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), jaridar Daily Trust.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Mawakin Buhari, Malam Yala ya ajiye aikin muƙamin SA na kakakin majalisar Kaduna

Banda asarar dukiya: Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 40 a Jigawa
Banda asarar dukiya: Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 40 a Jigawa Hoto: @GuardianNigeria
Source: Twitter

A halin da ake ciki, kungiyar ci gaban masarautar Hadeja (HEDA), ta danganta matsalar ambaliyar da ake samu duk shekara da gazawar gwamnatocin baya a jiha da ma tarayya.

Sun zarge su da rashin daukar kowani mataki don dakile ta.

Masarautar, wacce ke karkashin mazabar Jigawa ta arewa maso gabas, tana dauke da kananan hukumomi takwas da suka hada da; Hadejia, Kaugama, Auyo, Malammadori.

Sauran sune Birniwa, Gurin, Kirikasanma da Kafin Hausa.

Shugaban kungiyar, Alhaji Abdullahi Sarki Kafinta, wanda yayi jawabi ga ‘yan jarida a garin ya nuna takaicinsa matuka kan irin mawuyacin halin da jama’a da dama suka shiga.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tallafawa yankin da nau’o’in iraruwan shuka daban-daban da kuma ‘ya’yan kifaye da za a zuba a kududdufansu bayan ambaliyar.

Da yake martani kan lamarin a ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa da ambaliyar ta Hadeja wacce ta janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

Shugban kasar a wata sanarwa daga kakakinsa, Garba Shehu, ya yi jaje ga mutanen da ambaliyar ta ritsa da su, wanda a cewar rahoton da aka samu, ya lalata gonakin shinkafa sama da kadada 100,000.

KU KARANTA KUMA: Damfara: Shugaban KAROTA zai gurfana a gaban kotu

Buhari ya bayyana lamarin a matsayin babbar barazana.

Ya kuma ba wadanda abun ya rista da su tabbacin cewa gwamnati ba za ta yasar da su ba.

A gefe guda, mun ji cewa wasu fusatattun matasa a ranar Talata sun kai wa hadimin gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar da wasu jami'an gwamnatin jihar hari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel