‘Yan Majalisa su na so ayi fatali da zabin Aisha Umar a Hukumar PENCOM

‘Yan Majalisa su na so ayi fatali da zabin Aisha Umar a Hukumar PENCOM

- Shugaba Muhammadu Buhari ya na so Aisha Umar ta rike Hukumar PENCOM

- Wasu ‘Yan Majalisa sun ce lallai hakan ya sabawa dokokin kasa da na hukumar

- Wasu sun ce ya kamata sabuwar shugabar PENCOM ta fito ne daga yankin Kudu

Zaben da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na Misis Aisha Umar a matsayin shugabar hukumar PENCOM ya raba kan ‘yan majalisar dattawa.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa wasu sanatoci sun fito karara, sun nuna rashin amincewarsu da zaben Aisha Umar a kujerar shugabar PENCOM.

‘Yan majalisar sun nuna adawarsu ga wannan mataki da shugaban kasar ya dauka jim kadan bayan Ahmad Lawan ya karanto wasikar Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Buhari zai raba motoci a sakamakon karin farashin man fetur

Sanata Enyinnaya Abaribe ya yi magana a madadin fusatattun ‘yan majalisar, ya ce bai kamata a maye gurbin Chinelo Anohu-Amazu da Misis Umar ba.

Yayin da tsohuwar shugabar PENCOM, Chinelo Anohu-Amazu ta fito daga yankin Kudu maso gabas, Umar ta fito ne daga Arewa maso gabashin kasar.

Enyinnaya Abaribe mai wakiltar Abia, ya bayyana cewa wannan nadin da shugaban kasar ya ke nema ya yi, ya ci karo da dokokin da su ka kafa hukumar.

Sashe na 20(1) da na 21(1) da kuma (2) na dokar PENCOM, sun bukaci wanda zai maye gurbin shugaban hukumar ya fito daga yankin da na baya ya ke.

KU KARANTA: Shugaban Najeriya ya rubuta wasika zuwa ga Shugaban China

‘Yan Majalisa su na so ayi fatali da zabin Aisha Umar a Hukumar PENCOM
Buhari ya na so Umar ta zama Darektar PENCOM Hoto: BRT News
Source: UGC

A dalilin haka Sanatan na PDP ya ce dole wanda za ta gaji kujerar Amazu, ta fito daga Kudu maso gabas.

“Wannan ya ci karo da dokar hukumar PENCOM da tsarin kama-kama na gwamnatin Najeriya.”

Ahmad Lawan ya yi watsi da maganar Abaribe, ya ce a kai korafi gaban kwamtin da zai yi aikin.

Kwanaki kun ji cewa shugaban kasa ya sa an biya tsofaffin ma’aikatan NITEL/MTEL fiye da 11, 000 hakkokinsu na fansho, adadin kudin ya kai miliyan 800.

Hakan na zuwa ne shekara da shekaru bayan gwamnatin tarayya ta sallamesu daga bakin aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel