Allahu Akbar: Baturen ilimi na birnin tarayya Abuja, Marafa ya rasu

Allahu Akbar: Baturen ilimi na birnin tarayya Abuja, Marafa ya rasu

- Allah ya yiwa mukaddashin sakataren ilimi na birnin tarayya Abuja, Alhaji Umaru Marafa rasuwa

- Ministan babbar birnin tarayya, Malam Malam Muhammad Bello, ya nuna alhini a kan wannan rashi da aka yi

- Marigayin ya amsa kiran mahaliccinsa bayan dan jinya da yayi

Ministan babbar birnin tarayya, Malam Muhammad Bello, ya nuna bakin ciki a kan mutuwar mukaddashin sakataren ilimi, Alhaji Umaru Marafa, wanda ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a yammacin ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

Bello ya bayyana marigayin a matsayin jajirtacce kuma jami’i mai kwazon aiki wanda ya bayar da gudunmawa sosai a hukumar birnin tarayya.

Allahu Akbar: Baturen ilimi na birnin tarayya Abuja, Marafa ya rasu
Allahu Akbar: Baturen ilimi na birnin tarayya Abuja, Marafa ya rasu Hoto: Ogeneafrican
Source: UGC

Ya yi sharhi a kan tarin aiki da marigayin da tawagarsa a sakatariyar ilimi suke yi domin tabbatar da sake bude makarntun birnin tarayya cikin nasara a yayinda ake farfadowa daga annobar COVID-19, aridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yadda mayaƙan Boko Haram suka yi amfani da jaki wajen kai wa Gwamna Zulum hari

A wata sanarwa daga babban sakataren labaran ministan birnin tarayya, Anthony Ogunleye, ya ce: “Ministan birnin tarayyan na kuma mika ta’aziyya ga gwamnati da mutanen jihar Neja da masarautar Kontagora, wanda marigayi Umaru Marafa ya kasance yarima a cikinta.

“Ya yi addu’an jin kai ga mamacin sannan ya roki Allah ya ba iyalansa dangana na wannan babban rashi da suka yi.”

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Buhari ya yi manyan nade nade, ya aika wa majalisa da sunaye

A wani labarin kuma, mun ji cewa Allah ya yiwa tsohon babban alkalin jihar Kano, Justis Shehu Atiku rasuwa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shehu Atiku ya rasu ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba, bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

Kakakin bangaren shari’a na jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel