Kashe-kashe: Ana zargin ‘Yan Sanda da kashe mai zanga-zanga a Jihar Katsina

Kashe-kashe: Ana zargin ‘Yan Sanda da kashe mai zanga-zanga a Jihar Katsina

- Mutanen Garin Jibiya sun fita zanga-zanga a kan kashe-kashen da ake ta yi

- Mazauna garin sun ce an yi kwana da kwanaki ana kai masu hari a Katsina

- Tun ba yau ba, ana ta fama da matsalar rashin tsaro a Jihar Shugaban kasar

An rasa mutum daya daga cikin mazauna garin Jibiya da su ka shirya zanga-zanga a sanadiyyar matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin na jihar Katsina.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a jiya cewa al’ummar Jibiya sun yi zanga-zanga domin nuna rashin jin dadin abin da ke faruwa na yawaitar kashe-kashe.

Wajen wannan zanga-zanga, an harbe wani mutumi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Rahotanni sun ce an jami'ai sun kama mutane akalla 43 a jiyan

Ana zargin dakarun ‘yan sandan Najeriya da aka tura su lafar da wannan zanga-zanga ne su ka harbi wannan Bawan Allah a ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2020.

KU KARANTA: ACF sun sa wa Sojoji alamar tambaya saboda kai wa Zulum hari

Wani ‘danuwan marigayin wanda ya bayyana sunansa da Abdulhadi, ya yi magana da ‘yan jarida yayin da ya ke kuka, ya ce ‘yan sanda sun kashe masa ‘danuwa.

“Kanina ne, an kashe shi.” Inji Abdulhadi.

Wani mutumi da ya fito daga kauyen Daddara, mai suna Falalu Abba, ya bayyana cewa dole ta sa talakawan yankin su ka fita zanga-zanga domin nuna bacin ransu.

"A ranar Lahadi, kwana 39 kenan a jere, kullum sai an kai hari. Idan aka kira jami’an tsaro, sai su ki zuwa mutane sun gaji don haka su ka dauki doka a hannunsu.”

KU KARANTA: Jonathan da Buhari sun sa labule a kan juyin-mulkin kasar Mali

Kashe-kashe: Ana zargin ‘Yan Sanda da kashe mai zanga-zanga a Jihar Katsina
Hafsun sojoji da Buhari Hoto: This Day
Source: Twitter

Bayan Abba, wani mazaunin Jibiya, garin da ke kan iyaka da Kasar Nijar, Muhammad Bello, ya na cikin wadanda su ka fita wannan zanga-zanga da aka yi.

Shi ma Abba ya ce al’umma su na fuskantar hare-hare, amma babu abin da aka iya yi wa miyagun.

Dazu kun ji cewa Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari za ta raba motocin haya, domin a rage radadin karin kudin fetur da aka yi a farkon wannan watan.

George Akume ya ce hakan zai taimaka matuka wajen rage radadin talaucin da ake yi a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel