Ku sani: Dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta kama jarumin Kannywood, Naburaska

Ku sani: Dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta kama jarumin Kannywood, Naburaska

- Kwamitin kula da tsaftar muhalli da gwamnatin jihar Kano ta kafa, ta kama dan wasan Hausa, Mustapha Naburaska a karshen makon da ya gabata

- An gurfanar da jarumin a gaban kotun tafi-da-gidanka sakamakon keta dokar kwamitin na hana fita har sai karfe 10:00 na safe a duk ranar Asabar din karshen wata

- Sai dai jarumin na Kannywood ya ce rashin sani ne ya sa shi fitowa don halartan wata jana’iza

Shahararren jarumin nan na Kannywood wanda ya kware a fannin barkwanci, Mustapha Naburaska, ya shiga tarkon kwamitin tsaftar muhalli da gwamnatin jihar Kano ta kafa a karshen makon da ya gabata.

Jarumin wanda ya kasance mazaunin unguwar Tudun Wada da ke karamar hukumar Nasara ta jihar, ya gurfana a gaban kotun tafi-da-gidanka kan take dokar kwamitin tsaftar muhalli.

Kwamitin dai ya hana fita har sai karfe 10:00 na dace a duk ranar Asabar ta karshen wata.

Ku sani: Dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta kama jarumin Kannywood, Naburaska
Ku sani: Dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta kama jarumin Kannywood, Naburaska Hoto: mustaphanabraska
Asali: Instagram

A zantawa da yayi da manema labarai na gidan radiyon Freedom, Naburaska ya bayyana cewa rashin sani ne ya sanya shi fita domin halartan jana’izar wani rasuwa da aka yi.

KU KARANTA KUMA: Zan sauka daga Gwamna idan Amaechi ya nuna aiki ɗaya da yayi wa Rivers - Wike

Ya kuma bayyana cewa a yanzu ya fahimci cewa tsaftar muhalli ta doke duk wani uzuri.

An tattaro cewa Kotun ta ci tarar jarumin kudi naira dubu biyar kan keta dokar kwamitin na zama a gida don tsaftace muhalli.

Amma kuma jarumin ya nemi sassauci inda ta yi masa rangwamen biyan naira dubu uku.

A wani labarin kuma, Jarumin shirya fina-finai na Kannywood, Yakubu Mohammed, ya nuna dana sanin fitowa a wani fim din Nollywood na 'yan shi'a mai suna "Fatal Arrogance."

KU KARANTA KUMA: Yadda ake zaben Shugabanni a Musulunci inji Dr. Ahmad Gumi

Fitaccen jarumin nan na kudancin Najeriya, Pete Edochie ya fito a matsayin jagora a shirin fim din da akayi a jihar Enugu, wanda Anosike Kingsley Orji ya dauki nauyi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng