Yadda ake zaben Shugabanni a Musulunci inji Dr. Ahmad Gumi

Yadda ake zaben Shugabanni a Musulunci inji Dr. Ahmad Gumi

- Shehin Malami Ahmad Abubakar Gumi ya yi magana a kan nadin Shugaba

- Malamin ya ce hanya mafi sauki na zaben shugaba shi ne a tara ‘yan takarar

- Dr. Gumi ya ce a ba kowane damar ya fadi wanda ya ke so idan shi ya rasa

Babban malamin addinin nan, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana game da yadda ake zaben shugabanni idan ana da masu neman takara.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana hanya mai sauki da za a zabi shugaba wanda zai samu goyon bayan duk sauran abokan takararsa.

“A samu ‘yan takarar a tara su wuri guda. Kowanensu ya fadi sunan wani daga cikinsu a boye wanda za su so ya samu kujerar idan shi ya rasa.”

Gumi ya ke cewa: “Shi ke nan wanda ya fi samun kuri’u masu yawa a nan, ya zama shugaba.”

KU KARANTA: An yi rashi na Shehu Idris - Gumi

Bajimin malamin ya kara da cewa, kuma shugaban da aka samu, zai fi samun goyon bayan sauran.

Ahmad Abubakar Gumi ya yi wannan bayani ne a shafinsa na Facebook a karshen makon jiya, kusan mako guda da rasuwar Sarkin Zazzau, Shehu Idris.

Ko da cewa Malamin bai fito ya ambaci sunan gwamnati ko masu nada sabon Sarki a Zariya ba, wannan shawara da ya kawo za ta yi amfani sosai a Kaduna.

Gumi ya ce ta haka ne Othman ‘Dan ‘Affan- radiyallahu ‘anhu ya zama shugaban al’ummar Musulmai bayan Khalifan Manzon Allah, Umar ‘dan Khattab.

Yadda ake zaben Shugabanni a Musulunci inji Dr. Ahmad Gumi
Nasir El-Rufai, Dr. Ahmad Gumi da Atiku Hoto: Twitter/GovKaduna
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ina ma Mace ta zama Sarki - Misis El-Rufai

Malamin ya kara da cewa, “Idan har musulmai su ka rasa tsarin Shura, sun rasa wani jigo na shugabanci wanda zai iya jawo masu jin kunya a Duniya.”

Shehin ya karkare jawabinsa da jawo wata aya a cikin littafin Al-Qur’ani mai tsarki da ta ce: “Idan har ba mu komawa addinmu ba, za mu cigaba da bulinbintuwa ne. “

A game da sarautan Zazzau, kun ji cewa Yarima Manir Jafaru ya yi magana kan jita-jitar nada shi Sarki. Jafaru ya karyata hakan ne ta bakin San Turakin Zazzau.

Haka zalika kun ji cewa Turakin Zazzau ya dawo cikin lissafin ‘yan takaran kujerar Sarkin Zazzau.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng