Gwamnatin Tarayya za ta raba motocin haya, a rage radadin karin kudin fetur

Gwamnatin Tarayya za ta raba motocin haya, a rage radadin karin kudin fetur

- Gwamnati za ta raba motocin haya a dalilin karin kudin man fetur

- Wannan zai taimaka wajen rage radadin talauci da ake ciki a kasar

- Dr. George Akume ya ce za su ceto mutane miliyan 100 daga talauci

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kafa duk matakan da za ta bi wajen rabon motoci 2, 000 a yunkurin da ta ke yi na rage talauci a fadin kasar nan.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Ministan harkokin mususamman, Dr. George Akume, ya na wannan bayani a ranar Litinin, 29 ga watan Satumba, 2020.

George Akume ya bayyana haka ne a wajen taron da aka shirya tsakanin duka ma’aikatun gwamnatin tarayya a kan yadda za a rage talauci a kasa.

KU KARANTA: Kudin wuta: NLC da TUC sun fasa shiga yajin aiki bayan cin ma matsaya

Ministan ya ke cewa wannan ya na cikin shirin da gwamnati ta ke yi, ta karkashin ma’aikatarsa, na ceto mutanen Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci.

Sauran ma’aikatun da za a hada kai da su wajen wannan aikin raba motoci su ne na noma da cigaban karkara da kuma wasu hukumomin gwamnatin tarayya.

Akume ya ke cewa za a raba motocin ne ta karkashin kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya.

Gwamnatin Tarayya za ta raba motocin haya, a rage radadin karin kudin fetur
Taron Ministocin Gwamnatin Tarayya Hoto: Twitter/NGRPresident
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnoni sun maka Buhari a kotun koli

“Shirin ceto mutane daga cikin talauci ya dade cikin manufofin gwamnatin nan mai-ci ta shugaban kasa Muhammadu Buhari.” Inji George Akume.

“Idan za ku tuna, shugaban kasa a jawabinsa na ranar murnar farar hula ta shekarar 2019, ya ce idan aka samu shugabanci da niyya, za a iya cire mutane miliyan 100 daga talauci.”

Dr. Akume ya ce don haka za a cika wannan alkawari a sakamakon ci-bayan da annobar COVID-19 ta jawowa tattalin Duniya, tare da duba karin kudin mai da aka yi.

Dazu kuma kun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wasika zuwa ga Shugaban Sin, Xi Jinping domin taya shi murna.

Buhari ya ce kasar Sin ta taimaka matuka wajen gina abubuwan more rayuwa a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel