Batagari sun kaiwa jami'an kwastam harin kwanton bauna bayan sun kwace shinkafa

Batagari sun kaiwa jami'an kwastam harin kwanton bauna bayan sun kwace shinkafa

- Har yanzu iyakokin Najeriya na kan tudu a rufe suke tun shekarar 2019

- Sai dai, rufe iyakokin bai hana ma su fasa kwauri da sauran 'yan kasada cigaba da shigo da kayayyyaki ta barauniyar hanya ba

- Wasu batagari a jihar Ogun sun kaiwa jami'an kwastam hari a hanyarsu ta dawowa daga kwacen shinkafa a hannun ma su fasa kwauri

Rahotanni sun bayyana cewa wasu batagari da ake kyautata zaton cewa ma su fasa kwauri ne sun yi garkuwa da wani jami'in hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), A. K Usman tare da yin awon gaba da bindigarsa.

Lamarin ya faru ne bayan wata arangama tsakanin jami'an NCS na kwamand ta 1 a jihar Ogun da wasu ma su fasa kwaurin shinkafa zuwa Najeriya ta iyakarta da ke Oja Odan a karamar hukumar Yewa ta kudu.

Wani mutum mai matsaikaicin shekaru, Atanda Idowu Moses, ya rasa ransa sakamakon samun rauni bayan harasashin bindiga ya sameshi yayin da ake musayar wuta tsakanin jami'an NCS da ma su fasa kwauri.

Daily Trust ta rawaito cewa Moses tare da wani mutum guda daya suna aikine a cikin shagonsu ranar Asabar yayin da harsashi ya kufce ya zo ya sameshi.

Kafin mutuwarsa, Moses shine shugaban kungiyar ma su kera motoci ta Najeriya reshen Oja Odan.

KARANTA: Rochas ya bayyana ma su jawowa Buhari zagi a wurin 'yan Najeriya

Sai dai, kakakin rundunar hukumar kwastam na kwamand ta I, Hameed Oloyede, ya shaidawa Daily Trust cewa an kaiwa jami'an NCS harin kwanton bauna bayan sun kwace buhunhunan shinkafar waje 18 daga hannun 'yan sumogal.

Da ya ke bayyana hakan ranar Litinin, Oloyede ya bayyana cewa Moses ya rasa ransa ne sakamakon harbin da 'yan sumgol ke yi yayin da jami'an NCS su ka biyosu.

Batagari sun kaiwa jami'an kwastam harin kwanton bauna bayan sun kwace shinkafa
Hameed Ali
Asali: Depositphotos

A cewarsa, 'yan sumogal din sun fara yin garkuwa da wani jami'in NCS tare da kwace bindigarsa, wacce suka yi amfani da ita wajen yin harbin da ya zama sanadiyyar mutuwar Moses.

"Wasu batagari dauke da muggan makamai sun kai wa jami'anmu harin kwanton bauna yayin da su ke kan hayarsu ta dawowa daga kwacen shinkafa daga hannun wasu 'yan sumogal.

"Sun yi amfani da mugayen makamai da suka hada da bindigar baushe, kwalabe, duwatsu da wasu tarkacen asirai.

KARANTA: FG ta buɗe sabon shafin yanar gizo, ta ƙirƙiri manhajar wayar hannu - Pantami

"Sun kama jami'inmu tare da yin garkuwa da shi, sun yi ma sa dukan tsiya, sannan sun kwace bindigarsa, sun karar da alburusai 19 da ke cikinta tare da lalatata a karshe.

"Taimakon gaggawa da rundunar 'yan sanda ta kawo a kan lokaci ya yi matukar amfani, saboda sun samu nasarar kubutar da jami'anmu tare da gano bindigarsa da aka lalata bayan an karar da alburusan cikinta," a cewar Oloyede.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel