'Yan bindiga sun sace darekta a gwamnatin jihar Zamfara tare da wasu mutane 4

'Yan bindiga sun sace darekta a gwamnatin jihar Zamfara tare da wasu mutane 4

- Har yanzu 'yan bindiga na cigaba da kai hare-hare a wasu Jihohin arewa musamman Katsina, Sokoto, da Zamfara

- Hare-haren na cigaba da zuwa bayan rundunar soji ta kaddamar da atisayen HADARIN DAJI da SAHEL SANITY domin magance 'yan bindiga a jihohin uku

- Wasu 'yan bindiga sun sake kai hari kauyen Kanoma a karamar hukumar Maru ranar Litinin da safiyar ranar Litinin

A ranar Litinin ne wasu 'yan bindiga suka sace mutane biyar da suka hada wani darekta a gwamnatin jihar Zamfara.

'Yan bindigar sun sace mutanen ne a kauyen Kanoma da ke yankin karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Mazauna kauyen sun bayyana cewa 'yan bindigar sun dira kauyen da misalin karfe 2:00 na safe tare da yin awon gaba da darekta a ma'aikatar lafiya ta jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: A karo na biyu: Zanga-zanga ta sake barkewa a jihar Katsina

Majiyar Daily Trust ta sanar da ita cewa 'yan bindigar sun balle kofar gidan darektan kafin su samu damar kutsa kai cikin gidansa.

'Yan bindiga sun sace darekta a gwamnatin jihar Zamfara tare da wasu mutane 5
'Yan bindiga sun sace darekta a gwamnatin jihar Zamfara tare da wasu mutane 5
Asali: Twitter

"Bayan nan sun shiga gidan tsohon mataimakin magatakardar majalisar dokokin jiha tare da yin awon gaba da wasu daga cikin iyalinsa, sun kuma harbe wani mutum bayan sun yi garkuwa da makwabcinsa kafin su shige cikin daji.

DUBA WANNAN: APC ta yi babban rashi, tsohon gwamna ya sake komawa tsohuwar jam'iyyarsa PDP

"Su, 'yan bindigar sun taba aiko sakon cewa za su dauki mataki maras dadi idan aka kara taba wani dan Fulani idan ya zo gari cin kasuwa," kamar yadda mazaunin garin mai suna Ibrahim ya shaidawa Daily Trust.

Kokarin jin ta bakin SP Muhammad Shehu, kakakin rundunar 'yan sanda, domin jin ta bakinsa a kan kai harin bai samu ba har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng