APC ta tafka babbar asara a Kwara: Kotu ta soke nasarar dan majalisa, ta ba PDP

APC ta tafka babbar asara a Kwara: Kotu ta soke nasarar dan majalisa, ta ba PDP

- Kotun zabe ta tsige dan majalisa na APC a Kwara, Adam Rufai

- A ranar Litinin, 28 ga watan Satumba ne aka soke nasarar Rufai

- Kotun zaben ta kaddamar da PDP a matsayin wacce ta lashe zaben na cike gurbin

Kotun zabe ta tsige dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben cike gurbi na majalisar dokokin jihar Kwara, Adam Rufai.

Legit.ng ta rahoto cewa kotun zaben a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, ta soke nasarar Rufai a zaben cike gurbi na mazabar Patigi.

Kotun zaben ta kuma kaddamar da Salihu Mohammed Gada na Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbin na ranar 14 ga watan Maris.

Da take martani kan hukuncin, jam’iyyar APC reshen jihar Kwara, ta yi watsi da hukuncin kotun zaben wanda ya kaddamar da dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na Patigi da aka yi kwanaki.

Ta wallafa a shafinta na Twitter cewa: "APC reshen jihar Kwara ta yi watsi da hukuncin kotun zabe da ta kaddamar da dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na Patigi a majalisar dokoki."

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa har yanzu ba a nada sabon sarkin Zazzau ba, in ji masana tarihi

APC ta tafka babbar asara a Kwara: Kotu ta soke nasarar dan majalisa, ta ba PDP
APC ta tafka babbar asara a Kwara: Kotu ta soke nasarar dan majalisa, ta ba PDP Hoto: @MediaApc
Asali: Twitter

Ku tuna cewa kujerar ya zama babu kowa tun bayan da dan uwan Rufai, Saidu Ahmed, ya rasu a watan Disamban 2019, sakamakon rashin lafiya da yayi.

Kotun zaben ta yi bayanin cewa hukuncin ya kasance kan banbanci da aka samu tsakanin sunan Adam da Adama da ke kan satifiket din dan takarar na APC.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zanga ta sake barkewa a jihar Katsina

APC Kwara ta yi korafin a wata sanarwa daga sakataren labaranta, Folaranmi Aro, a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba.

Taken jawabin shine, 'APC ta yi watsi da hukuncin kotun zabe a kan Patigi, za ta daukaka kara... ta ce hukuncin take muradin mutane ne.'

Aro ya yi korafin cewa PDP bata kira kowani shaida daga hukumar jarrabawa ba, domin tabbatar da ikirarinta na cewa ba dan takarar APC bane mamallakin wannan satifiket da ya gabatar don zaben ba.

A wani labarin, mun ji cewa maganar sake takarar Dr. Goodluck Jonathan a zabe mai zuwa ta na kara karfi kamar yadda jaridar Vanguard ta bayyana a farkon makon nan.

Rahotanni su na zuwa cewa wasu manyan ‘yan siyasa daga Arewacin Najeriya su na kokarin farfado da takarar Goodluck Jonathan a 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng