Zanga-zanga ta sake barkewa a jihar Katsina

Zanga-zanga ta sake barkewa a jihar Katsina

- Matasa sun sake fitowa domin gudanar da zanga-zanga a kan tabarbarewar tsaro a sassan jihar Katsina

- An rasa ran mutum guda yayin da wasu mutane da dama suka samu raunuka yayin zanga-zangar da mutane daga kauyuka da dama suka gudanar

- Wannan ba shine karo na farko da matasa suka fara gudanar-gudanar da zanga-zanga domin nuna bacin ransu a kan halin rashin tsaro ba a jihar Katsina

Wasu fusatattun matasa sun sake gudanar da zanga-zangar nuna fushinsu a kan yadda har yanzu 'yan bindiga ke cigaba da kai musu hare-hare a garuruwansu.

Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun tare babbar hanyar da ta taso daga Jibiya zuwa birnin Katsina.

Radiyon Freedom da ke Kano ta wallafa cewa wani matashi ya mutu yayin da wasu da yawa suka samu raunuka a lokacin zanga-zangar.

DUBA WANNAN: Labarin ƙarya ne: Elrufai ya magantu kan karɓar sunaye daga masu zaɓen sarkin Zazzau

A cewar rahoton da Freedom ta wallafa, dandazon mutane da suka fito daga kauyuka fiye da goma sun yi gangami domin gudanar da zanga-zangar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, DSP Gambo Isa, ya tabbatar da faruwar zanga-zangar.

Zanga-zanga ta sake barkewa a jihar Katsina
Gwamna Masari yayin wani sulhu da 'yan bindoga a jihar Katsina
Asali: Twitter

Sai dai, ya bayyana cewa jami'an rundunar 'yan sanda suna kokarin shawo kan zanga-zangar.

Wannan ba shine karo na farko da matasa suka gudanar da zanga-zanga a kan rashin tsaro ba a jihar Katsina.

DUBA WANNAN: Kano: Sunayen mutane 8 da ke takarar neman kujerar shugaban jami'ar YUMSU

Jami'an tsaro sun kama jagororin matasan da suka shirya wata zanga-zanga kwatankwacin irin wannan a baya a jihar Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel