‘Yan Arewa su na tunanin su bi bayan Goodluck Jonathan a zabe mai zuwa

‘Yan Arewa su na tunanin su bi bayan Goodluck Jonathan a zabe mai zuwa

- An fara sabon lissafin Goodluck Jonathan ya sake dawowa kan mulki

- Daga cikin masu wannan shiri har da wani tsohon Gwamna a Arewa

- Ana ganin cewa mulkin Goodluck Jonathan zai hada kan ‘Yan Najeriya

Maganar sake takarar Dr. Goodluck Jonathan a zabe mai zuwa ta na kara karfi kamar yadda jaridar Vanguard ta bayyana a farkon makon nan.

Rahotanni su na zuwa cewa wasu manyan ‘yan siyasa daga Arewacin Najeriya su na kokarin farfado da takarar Goodluck Jonathan a 2023.

Wadannan ‘yan siyasa na yankin Arewa su na ganin mulkin Goodluck Jonathan zai kawo hadin-kai.

A na su hangen, kusoshin siyasar su na ganin za a kafa gwamnatin hadin-kai a karkashin Jonathan bayan Muhammadu Buhari ya kammala mulki.

KU KARANTA: Buhari da Jonathan sun sa labule a Aso Villa

Wani gwamnan yankin Arewa maso gabas ya na cikin masu wannan shiri. Gwamnan ya yi aiki da Jonathan a lokacin da ya ke kan kujerar mulki.

‘Yan siyasan Arewa su na neman wanda za a tsaida daga Kudancin Najeriya da za su amince da mulkinsa bayan wa’adin shugaba Buhari ya cika.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Arewa ba za ta goyi bayan mulki ya koma Kudu maso gabashin kasar ba, amma za su iya bin bayan Jonathan.

Ya ce: “Idan Jonathan ya tsaya takara, mutanen Kudu maso kudu ba za su yi masa adawa ba.”

KU KARANTA: ‘Yan gida daya sun samu kujerar Minista da mukamai 5 a Gwamnatin Buhari

‘Yan Arewa su na tunanin su bi bayan Goodluck Jonathan a zabe mai zuwa
Goodluck Jonathan wajen kamfe Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Muddin Jonathan ya hau mulki, ‘yan siyasar yankin su na tunanin gwamnatinsa ba za ta murkushe su ba, za a dama da su kamar yadda aka yi a baya.

Wata dabara kuma ita ce mulki zai iya sake komawa Arewa a 2027 da zarar wa’adin Jonathan ya cika.

Ko da Goodluck Jonathan ya musanya shirin fitowa takarar shugaban kasa nan gaba, rahoton na makon nan ya ce kiran da ake yi masa ya yi karfi.

Idan za ku tuna daga cikin moriyar da Arewa ta samu a gwamnatin Jonathan tsakanin 2010 da 2015 akwai nadin mukamai da makarantu a yankin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel