Ba ruwan Boko Haram: Waɗanda suka kaiwa tawagar Zulum hari sun fito sun magantu

Ba ruwan Boko Haram: Waɗanda suka kaiwa tawagar Zulum hari sun fito sun magantu

- Kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai wa tawagar motocin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum

- A ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba ne dai aka kai wa motocin Zulum hari a hanyarsa ta dawowa daga Baga

- Sai dai babu tabbacin ko gwamnan na tare da tawagar nasa a lokacin da yan ta’addan suka kaddamar da harin

Kungiyar ta’addanci da ke ikirarin jihadi sun sake kai farmaki ga tawagar Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a lokacin da suke komawa Maduguri, babbar birnin jihar.

Gwamnan ya tsallake rijiya da baya a harin da suka kai a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba.

Sai dai babu wani tabbaci da ke nuna ko gwamnan na cikin tawagar.

KU KARANTA KUMA: Kwanaki 8 babu sabon sarki: Ana zaman jiran tsammani a garin Zazzau

Harin ya faru ne kimanin kwanaki biyu bayan yan Boko Haram sun far ma gwamnan a yankin Baga, lamarin da yayi sanadiyar rasa rayuka da dama ciki harda sojoji da yan sanda.

Ba ruwan Boko Haram: Waɗanda suka kaiwa tawagar Zulum hari sun fito sun magantu
RBa ruwan Boko Haram: Waɗanda suka kaiwa tawagar Zulum hari sun fito sun magantu Hoto: @BBC
Asali: Twitter

Sai dai kuma a yanzu haka, kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Zulum ya ziyarci Baga a kokari da gwamnatinsa ke yi na mayar da dubban yan gudun hijira gidajensu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Mayaƙan Boko Haram sun sake kaiwa tawagar Gwamna Zulum hari ranar Lahadi

A baya mun kawo maku cewa, Jami'an tsaro 15 suka rasa rayukan su ranar juma'a, 25 ga watan Satumba, sakamakon harin da yan Boko Haram suka kai wa tawagar gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.

Mutane da dama sun ji munanan raunika sakamakon harin da aka kai tsakanin Monguno da Baga.

Yan sanda 8, sojoji 3 da kuma CJTF guda 4 sun rasa rayukansu sakamakon harin, shafin Lina Ikeji ya wallafa.

A ranar lahadi 27 ga watan Satumba, wani kwamandan CJTF, Mu'azu Alhaji Misiya, ya wallafa hotunan jami'an tsaron da suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka ji raunuka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel