Sarautar Zazzau: Watakila ‘Dan Sarki Shehu Idris, Turaki ya gaji Mahaifinsa

Sarautar Zazzau: Watakila ‘Dan Sarki Shehu Idris, Turaki ya gaji Mahaifinsa

- Akwai yiwuwar Turakin Zazzau, Aminu Shehu Idris ya zama Sarkin Zazzau

- Turaki Aminu ya na cikin ‘yan takarar da aka aikawa Gwamnatin Kaduna

- Abu ne mai matukar wahala ‘Da ya gaji Mahaifinsa a Masarautar Zazzau

Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris zai iya darewa kan kujerar Sarkin Zazzau da yanzu ta ke ajiye bayan rasuwar Shehu Idris.

Jaridar The Guardian ta bayyana cewa akwai sunan Aminu Shehu Idris a cikin jerin ‘yan takarar da aka aikawa gwamnatin jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce masu zaben sabon Sarki a Zariya sun turawa Nasir El-Rufai sabon jerin sunayen masu harin kujerar sarautar Zazzau.

Ana sa ran cewa mai girma gwamna Nasir El-Rufai zai fitar da Sarki bayan ya yi la’akari da jeringiyar ‘yan takarar da aka kawo masa.

KU KARANTA: An fara yada cewa Yarima Manir Jafaru ne zai gaji Sarki Shehu Idris

Jaridar ta ce babu sunan Magajin Garin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli a cikin sunayen ‘yan takarar da masu zaben Sarki su ka turawa gwamna.

Akwai kishin-kishin cewa gwamnatin Kaduna ta na fifita takarar Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.

Aminu Shehu Idris shi ne babban ‘dan tsohon Sarki Shehu Idris wanda ya rasu a ranar Lahadi bayan ya shafe shekaru 45 a gadon sarauta.

Gidajen Katsinawa, Bare-bari, Mallawa da kuma Sullubawa ne su ke mulkin kasar Zazzau.

Sarautar Zazzau: Watakila ‘Dan Sarki Shehu Idris, Turaki ya gaji Mahaifinsa
Tsohon Sarkin Zazzau Shehu Idris Hoto: Shehu Idris
Source: Getty Images

KU KARANTA: El-Rufai ya kusa gama karance-karance kan nadin sabon Sarki

Turakin Zazzau ya fito ne daga gidan Katsinawa, tattaba-kunne ne na tsohon Sarki Sambo, Jikan Malam Abdulkareem Bakatsine da ya yi mulki.

Babban ‘dan tsohon Sarkin ya karanta ilmin tattali ne, kuma ya na aiki ne a kamfanin NNPC.

Hadimin gwamna, Muyiwa Adekeye, ya tabbatar da an aikawa gwamnati sunayen ‘yan takara. Ya ce gwamnati za ta bi sannu wajen zaben sabon Sarki.

A jiya kun ji cewa, an cusa sunan Ahmed Nuhu Bamalli cikin masu neman kujerar Sarki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel