Harin zaben 2023: Kwamitin ɗinke ɓarakar PDP ya gana da Babangida a Minna

Harin zaben 2023: Kwamitin ɗinke ɓarakar PDP ya gana da Babangida a Minna

- Mambobin kwamitin ɗinke ɓaraka ta PDP sun ziyarci Ibrahim Babangida a Minna

- Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ne yayi masu jagora a ranar Asabar, 26 ga watan Satumba

- Mohammed ya ce sun kai masa ziyara ne domin sanin yadda za su bunkasa jam'iyyarsu gabannin 2023

Mambobin kwamitin sulhu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Asabar, 26 ga watan Satumba, sun gana da tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida.

Channels TV ta ruwaito cewa Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya fada ma manema labarai a filin jirgin sama na mina cewa sun yi ganawar ne domin samo dabaru kan yadda za a kai jam’iyyar gaba.

Legit.ng ta tattaro cewa Mohammed ya ce kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ne ya kafa wannan kwamitin domin ganin yadda PDP za ta habbaka nasarorin kwanan nan da ta yi a zabuka.

KU KARANTA KUMA: Ba ruwan Buhari: Bashir Ahmad ya magantu kan zargin amfani da jirgin FG a shagalin bikinsa

Harin zaben 2023: Kwamitin ɗinke ɓarakar PDP ya gana da Babangida a Minna
Harin zaben 2023: Kwamitin ɗinke ɓarakar PDP ya gana da Babangida a Minna Hoto: Channels TV
Source: Twitter

Sauran mambobin da suka ziyarci Babangida sun hada da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da dan takarar Shugaban kasa na PDP a zaben 2019, Kabiru Turaki (SAN).

Jiga-jigan na PDP wadanda tsohon gwamnan jihar Neja, Muazu Babangida Aliyu ya yi wa jagora, sun isa filin jirgin sama na Minna cikin wani jirgi da aka yo shata mai lamba N604WL da karfe 1:15 na rana.

Bala Mohammed ya ce:

“Mun zo aiwatar da umurnin kwamitin masu ruwa da tsaki na duba matsaloli da kalubalen PDP gaba daya da kuma yadda za mu bunkasa sa’armu, ta yadda za mu yi gaba, fitowa daga tarin kaye muka sha a 2019 da martaba da tawali’u, ta yadda za mu tafiyar da kanmu da kuma samar da shugabanci da ake bukata domin ci gaban wannan kasa.

“PDP ce muradin kasar nan saboda mun koyi darasi daga kura-kuranmu na baya sannan mun amsa laifinmu, kuma kun ga abunda ya faru a Edo. Sannan da izinin Allah, za mu lashe Ondo, ba ta hanyar tursasawa da girman kai ba, illa ta hanyar aiki mai kyau.

KU KARANTA KUMA: Kalli sabon hoton biloniyan Najeriya, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina da yaransa mata su 16

“Kuma wannan ne dalilin da yasa kwamitin masu ruwa da tsaki, karkashin jagorancin Uche Secondus, ya kafa wannan kwamitin domin sake duba abubuwan da suka haddasa faduwarmu a 2019 da kuma ganin yadda za mu bunkasa nasarorin da muke samu zuwa yanzu a siyasar Najeriya."

A wani labarin, Gwamna Matawalle ya mika sakon godiyarsa ga matashin da yace zai yi tattaki dominsa amma ya dakatar dashi daga tafiyar mai cike da hadari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel