Ba ruwan Buhari: Bashir Ahmad ya magantu kan zargin amfani da jirgin FG a shagalin bikinsa

Ba ruwan Buhari: Bashir Ahmad ya magantu kan zargin amfani da jirgin FG a shagalin bikinsa

- Mai ba shugaban kasa shawara a kafar zumuntan zamani, Bashir Ahmad, ya karyata rade-radin cewa an yi amfani da jirgin shugaban kasa a shagalin bikinsa

- Bashir ya ce mota suka bi zuwa Katsina, Kano da Abuja daga shi har abokansa

- Ya ce hotonsu da aka gani a gaban jirgin shugaban kasa ya kasance lokacin da suka ziyarci wakilan shugaban kasa a filin jirgin sama

Bashir Ahmad, hadimi Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi watsi da rade-radin da ke ikirarin cewa ya yi amfani da jirgin Shugaban kasa a bikinsa.

Da farko dai mun ji yadda Ahmad ya angwance da amaryarsa Naeemah Junaid Bindawa, a jihar Katsina, a ranar Juma’a, 25 ga watan Satumba.

Yan sa’o’i bayan bikin, sai wani rahoto ya dingi yawo a yanar gizo inda aka zargi Buhari da cin mutuncin kujerarsa ta hanyar tura jirgin Shugaban kasa don bikin hadimin nasa.

Ba ruwan Buhari: Bashir Ahmad ya magantu kan zargin amfani da jirgin FG a shagalin bikinsa
Ba ruwan Buhari: Bashir Ahmad ya magantu kan zargin amfani da jirgin FG a shagalin bikinsa Hoto: The Cable
Source: Twitter

Amma da yake martani a shafin Twitter, hadimin Shugaban kasar ya ce rahoton ba gaskiyar ainahin abunda ya faru bane.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sake kashe wani babban kanal din soji a Katsina

Ya ce sabanin rahoton, shi da abokansa sun tafi Katsina daurin auren ne a mota sannan suka dawo Kano bayan daurin auren duk a mota.

Ahmad ya kara da cewa ya kuma koma Abuja tare da abokansa a cikin mota bayan an kammala komai na bikin.

Ya ce hoton da aka gani nasa da abokansa suna tsaye a gaban jirgin shugaban kasa ya kasance lokacin da suka ziyarci filin jirgin sama domin tarban wakilan shugaba Buhari a taron.

“Bashir Ahmad da abokansa sun je Katsina a ranar Alhamis ta hanyar mota, sannan suka garzaya Kano bayan daurin aure a ranar Juma’a kuma sun bar Kano zuwa Abuja duk a mota bayan shagulgulan bikin. Wannan lokacin da na jagoranci abokaina ne domin tarban wakilan @MBuhari a filin jirgin sama,” ya rubuta.

KU KARANTA KUMA: Kalli sabon hoton biloniyan Najeriya, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina da yaransa mata su 16

A baya mun kawo maku cewa, a ranar Juma'a, Allah ya kaddara, aka daura auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar kafofin sada zumunta, tare da amaryarsa, Naeemah.

An daura auren Bashir da Naeemah a babban Masallacin G.R.A, jihar Katsina, inda dubunnan mutane suka taru don shaida wannan aure.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel