Manyan abubuwa 4 da suka faru bayan rasuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris

Manyan abubuwa 4 da suka faru bayan rasuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris

- Ana ci gaba da zuba ido don ganin wanda zai dare kujerar sarkin Zazzau

- Gidan Mallawa, Gidan Barebari, Gidan Sullubawa da kuma gidan Katsinawa ne gidaje hudu da ke sarautar Zazzau

- Masu zaben sabon sarki dai sun killace kansu

A yanzu haka kallo ya koma sama a masarautar Zazzau inda ake jiran ganin wanda zai gaji marigayi Sarki Abdullahi Shehu Idris.

Tun bayan rasuwar Sarki Idris a ranar Lahadi ake ta hasashe kan wanda ka iya maye gurbinsa wajen zama sabon sarki.

Da dama dai na ganin akwai tafiyar hawainiya a tsarin nada sabon sarkin.

A yadda yake a tsarin sarautar Zazzau, ana zabar sabon Sarki ne daga gidajen masarautar guda huda da suka hada da; Gidan Mallawa, Gidan Barebari, Gidan Sullubawa da kuma gidan Katsinawa.

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ne ke da alhakin zabar wanda zai zama Sarkin Zazzau, daga cikin yayan gidan masarautar ya Zazzau wanda masu nadin Sarki za su aike masa.

Manyan abubuwa 4 da suka faru bayan rasuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris
Manyan abubuwa 4 da suka faru bayan rasuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris Hoto: @bbchausa
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe

Tun bayan rasuwar Sarki Idris, abubuwa da dama sun wakana wanda daga cikinsu akwai:

1. Masu zaben sabon sarki sun kebe kansu

Kamar yadda yake a al’ada, masu zaben sarki kan killace kansu na tsawon wani lokaci inda za su yi nazari da tantancewa kafin majalisarsu ta zabi sarki.

A wannan yanayi, ana karantowa yan majalisar ka’idojin zabar wanda zai zama sarki wanda suka hada da:

Ya zama bai taba yin laifi wanda hukuma ta damke shi ko ta hukunta shi ba.

Ya zamo ya taba rike matsayi na sarauta ko hakimta a masarautar Zazzau.

Ya zamo ba tsoho tukuf ba.

A tabbatar da ya fito daga gidajen sarautar yankin hudu.

Daga nan sai a tantance sunaye a majalisar zabar sarki, sannan sai a aike wa gwamna da sunayen kafin sanar da sabon sarki.

2. Martanin El-Rufai yayinda yake jiran sunaye daga masu zaben sarki

A yayinda ake ta jiran sunaye daga masu zaben sarki, Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa yana karanta wani littafin Bature kan zaben sabon sarkin Zazzau.

El-Rufai ya ce littafin wanda ke jawabi kan zaben sarakinan Zazzau daga 1800 zuwa 1950 zai shige masa gaba wajen yanke hukuncin zaben sabon sarkin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Masu zaben sarki sun aikewa gwamna El-Rufa'i sunayen mutane 3 (Kalli makin da kowanni ya samu)

3. Halin da Gwamnan Kaduna ya shiga

Har ila yau bayan samun labarin rasuwar Sarki Shehu Idris, El-Rufai ya ce bai sake samun bacci ba sai dai in ya sha magani. Ya ce hakan ta kasance ne saboda bakin ciki.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a wajen taron addu’an uku na marigayin.

4. Addu’ar kwanaki uku da rasuwar sarkin Zazzau

An gudanar taron addu’a na kwanaki uku da rasuwa sarkin Zazzau, lamari da ya samu halartan manyan shugabannin Najeriya.

Daga cikin manyan da suka Hallara harda tsoffin shugabannin kasa, Shugabannin majalisar dokokin tarayya, sarakuna da kuma manyan jami’an gwamnati.

Hakazalika masarautar Zazzau na ta samun sakkonin ta’aziyya na wannan babban rashi daga lungu da sako.

A gefe guda, Kwamred Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa game da wanda ake sa ran cewa zai zama sabon Sarkin Zazzau.

Shahararren ‘dan siyasar ya yi wani magana a kaikaice a shafinsa na Facebook, yayin da ake jiran sanarwar sabon sarki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel