Hasken Fadan Kano ya na sa rai Ahmad Bamalli ya gaji Sarki Shehu Idris

Hasken Fadan Kano ya na sa rai Ahmad Bamalli ya gaji Sarki Shehu Idris

- Tsohon Hasken Fadar Kano ya na so Ahmad Bamalli ya yi Sarkin Zazzau

- Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya na cikin masu neman kujerar Sarki

- Bamalli ya fito ne daga gidan Mallawa wadanda su ke da gadon sarauta

Hasken fadar tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya koma fadanci a gidan Mallawan Zariya, inda ake shirin nada sabon sarki.

Bayan rasuwar Mai martaba Shehu Idris, an fara maganar wanda zai gaji kujerarsa, daga ciki akwai sunan Magajin Gari, Ahmad Nuhu Bamalli.

Hasken fadan Kano ya na cikin wadanda su ke addu’ar Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya samu wannan kujera da kakanninsa su ka rike.

KU KARANTA: Takarar Zazzau ta na tsakanin Aminin Buhari da na-kusa da El-Rufai

Da ya ke yi wa Ahmad Nuhu Bamalli kirari a ranar Laraba, 24 ga watan Satumba, 2020, marokin ya ce Mallawa ba su bin wani, sai dai a bi su.

Ambasada Bammali ya fito ne daga gidan Mallawa, wadanda su ka fara karbar tutar sarautar kasar Zazzau daga hannun Shehu Usman Danfodio.

Marokin ya kambama asalin Ahmad Nuhu Bamalli da cewa shi ne Jikan Sarakunan Zazzau Malam Musa, Sidi, Abubakar da Sarki Ali ‘Dan Sidi.

Hasken Fadan Kano ya na sa rai Ahmad Bamalli ya gaji Sarki Shehu Idris
Hasken Fadan Kano da Ahmad Bamalli Hoto: Youtube/The Big Chill
Source: UGC

Haka zalika Basaraken jika ne a wajen Madaki Ali, Magajin Gari Zakari, Wambai Zubairu, ‘Dan Galadima Abbas, da kuma Wali Halliru.

KU KARANTA: Halin da kadarorin Muhammadu Sanusi II su ke ciki a fadar Kano

A nasabar Bammali akwai Madaki Sa’idu kamar yadda tsohon hasken fadar Kano ya bayyana.

Da ya ke fadanci, tsohon yaron Sarkin ya bayyana cewa ba zai bar kasar Zariya ba, ya kuma yi addu’a Ubangiji ya takaitawa Magajin gari jira.

Dama can ana rade-radin akwai manyan da ke kokarin ganin gwamnatin Kaduna ta nada Bammalli a matsayin magajin Marigayi Shehu Idris.

Kwanaki mun kawo maku wani tsohon bidiyon Shehu Idris ya na magana da Sarki Aminu Ado a kan mahaifinsa, marigayi Ado Bayero.

A Ranar 20 ga watan Satumban 2020, Sarkin Zazzau, Shehu Idris ya rasu a asibiti a Kaduna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel