Takarar shugaban ƙasa 2023: Manzo Ayodele ya faɗi abunda zai faru da Tinubu

Takarar shugaban ƙasa 2023: Manzo Ayodele ya faɗi abunda zai faru da Tinubu

- Primate Ayodele ya kaddamar da cewar Asiwaju Tinubu zai zamo shugaban kasar Najeriya nagari

- Babban faston ya bayyana cewa Tinubu na da abunda ake bukata don shugabantar kasar

- Sai dai Ayodele ya shawarci jigon na APC da ya kula da lafiyarsa

Biyo bayan rade-radi da ake yi game da kudirin tsohon gwamnan jihar Lagas kuma babban jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu na son takarar kujerar shugaban kasa a 2023, wani babban fasto, Primate Ayodele, ya fitar da sabon hasashe kan haka.

A wata hira da jaridar Tribune tayi da shi, malamin ya bayyana kudirin Tinubu na son zama shugaban kasar Najeriya a matsayin ci gaba mai kyau a tsarin siyasar kasar.

Legit.ng ta tattaro cewa Tinubu na da abunda ake bukata don jagorantar Najeriya cikin nasara, inda ta kara da cewa zai zamo shugaba nagari ga kasar.

Takarar shugaban ƙasa 2023: Manzo Ayodele ya faɗi abunda zai faru da Tinubu
Takarar shugaban ƙasa 2023: Manzo Ayodele ya faɗi abunda zai faru da Tinubu Hoto: The Eagle Online/@GuardianNigeria
Asali: Twitter

Sai dai, Primate Ayodele, ya shawarci jigon na APC da ya kula da lafiyar jikinsa, cewa Allah ne kadai zai iya barinsa ya kai 2023 da bayan ta.

KU KARANTA KUMA: Na yi farin cikin shan kaye a zaben gwamnan Oyo a 2019 - Dan takarar APC

Ya ce:

“Shirin Tinubu na zama shugaban kasa abune mai kyau. Yana da abunda ake bukata. Amma ya je ya kula da lafiyarsa. Ya kula da lafiyar jikinsa. Allah ne kadai zai iya barin Tinubu ya ga 2023 da bayanta. Ina kaunarsa; Ina son taimaka masa da addu’o’i. Zai kasance shugaban kasa na gari. Amma ba lallai ne lafiyarsa ya bari hakan ya faru ba.”

Da yake magana kan zaben gwamnan Ondo mai zuwa, malamin ya bukaci Gwamna Rotimi Akeredolu da ya hana idonsa bacci yayinda ya jaddada cewa hadiman gwamnan za su ci amanarsa a zaben.

Primate Ayodele ya kara da cewa:

“Ya zama dole Akeredolu ya hana idanunsu bacci. Akwai sauran rina a kaba. Yayi aiki; wasu daga cikin mutanen da ke kewaye da shi za su daba masa wuka a baya. Idan ba a yi hankali ba, wadanda suke ikirarin goyon bayansa za su koma bayan daya daga cikin yan takarar da ke adawa da shi. Yana bukatar mutane masu biyayya saboda kada su dakile nasararsa.”

Primate Ayodele ya shawarci Akeredolu da ya sake dabaru, cewa idan zai iya aiki kan kamfen dinsa da mayar da hankali, zai dawo a karo na biyu.

A gefe guda, wata kungiyar siyasa mai suna BAT 23, ta kaddamar da yakin neman zabe da kuma tattara masoya ga shugaban jam'iyyar APC, Bola Tinubu a zaben shugabancin kasa da ke zuwa na 2023 a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta dakatad da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi

An gano cewa, Tinubu na kokarin fitowa takarar zaben shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC a kasar nan.

Shugaban kungiyar, Umar Inusa, a yayin kaddamar da fara yakin neman zaben a Abuja a ranar sati, ya ce BAT 23 ta hada da dukkan magoya bayan Tinubu daga jihohi 36 na kasar nan tare da birnin tarayya, Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel