Bidiyo: Harin da sojoji suka kai wa 'yan Boko Haram a Bula Sabo da Dole a Borno
- Sojojin Saman Najeriya, NAF, sun kai hari mabuyar 'yan ta'addan Boko Haram da ke Bula Sabo da Dole a jihar Borno
- Sojojin sun yi amfani da jiragen yaki da jirage masu saukan ungulu sun yi wa 'yan ta'addan luguden wuta inda suka kashe da dama suka lalata gine-ginen
- Sojojin na NAF sun kai harin ne bayan samun ingantattun rahotannin sirri da ya tabbatar wasu kwamandojin Boko Haram da mayaka na zaune a gidajen
Dakarun sojojin saman Najeriya na musamman na Operation Lafiya Dole sun lalata mabuyar 'yan ta'addan Boko Haram sannan sun kashe da dama cikinsu a Bula Sabo da Dole a jihar Borno.
Sun samu nasarar yin hakan ne sakamakon hare-haren da suka kai da jiragen yakin sama a ranar 23 ga watan Satumba don kaddamar da sabon atisaye mai suna 'Hail Storm 2' da aka kaddamar don tarwatsa 'yan ta'addan Boko Haram da ke Tafkin Chadi da Dajin Sambisa.
DUBA WANNAN: APC ta dakatar da hadimin Buhari, surukin Tinubu da wasu mutane takwas
Wannan na cikin sanarwar da kakakin hedkwatar tsaro na kasa, Manjo Janar John Enenche ya fitar a shafin hukumar na Twitter a ranar Juma'a 25 ga watan Satumba.
Ya ce an kai hare-haren ne bayan samun sahihan bayannan sirri da ke tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun samu mafaka a wasu gine-gine da ke dajin inda wasu kwamandojinsu ke buya.
"An kai harin a Bula Sabo ne bayan sahihan bayannan sirri sun tabbatar kwamandojin Boko Haram na zaune a gine-ginen. Hakan yasa aka aike da jiragen yaki da jirage masu saukan ugulu suka tarwatsa gidajen tare da kashe wadanda ke ciki.
KU KARANTA: Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi
"Kazalika, an kai hari a Dole da ke Yale-Kokiwa kusa da Dikwa saboda 'yan ta'addan na amfani da wurin don tsara yadda za su kai hari a garuruwan da ke makwabtaka da garin. Jiragen yakin NAF sun yi luguden wuta a ginin tare da kashe mayakan 'yan ta'addan da dama," in ji Enenche.
Ga bidiyon harin a kasa:
A wani labarin, Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.
Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng