Matsalar tsaro: ‘Yan Majalisar Birtaniya sun sanar da Commonwealth halin Najeriya

Matsalar tsaro: ‘Yan Majalisar Birtaniya sun sanar da Commonwealth halin Najeriya

- Wasu ‘Yan Majalisar Birtaniya sun aika takarda gaban Shugabar Commonwealth

- ‘Yan Majalisa 18 su ka sa hannu a wasikar, su ka ce ana kashe mutane a Najeriya

- Takardar ta na ikirarin cewa Gwamnatin Tarayya ma-ci ta gaza kawo zaman lafiya

Wasu daga cikin ‘yan majalisar kasar Birtaniya sun aika takarda zuwa ga kungiyar Commonwealth a game da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita.

‘Yan majalisa 18 sun aika wannan takarda ne ga shugabar Commonwealth ta kasashen renon kasar Birtaniya, Patricia Scotland a ranar 14 ga watan Satumba, 2020.

Jaridar The Cable ta ce ‘yan majalisar Birtaniyan sun sanar da kungiyar gazawar gwamnatin tarayya na kare rayuka da kuma dukiyoyin mutanen Najeriya.

Rashin sauke wannan nauyi na kare jinanan ‘yan kasar ya ci karo da rantsuwar da Najeriya ta dauka a matsayinta na kungiyar kasashen da Birtaniya ta rena.

KU KARANTA: Mutane 3188 aka kashe a Najeriya a shekarar 2019

Wadannan ‘yan majalisa sun dogara da wani rahoto da kungiyar Ingila mai suna All-Party Parliamentary Group ta fitar a kan kashe-kashen da ake yi a Najeriya.

Kungiyar APPG ta ce ana kashe dubunnan ‘yan farar hula a kasar Afrikan, tare da zargin cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta na da sakaci wajen wannan rikicin.

‘Yan majalisar su na so Commonwealth ta binciki kashe-kashen da ake yi, sannan akalla ta dauki matakin kare al’umma, da kuma tallafawa wadanda lamarin ya shafa.

Bugu da kari, ‘yan majalisar sun bukaci kungiyar Commonwealth ta sake gidajen da aka ruguza.

KU KARANTA: An kama wani gawurtaccen 'Dan bindiga a Jos

Wasikar ta ce: “Gazawar gwamnati na kare ‘yan kasarta, cin karo ne da nauyin da ke kanta a karkashin dokar kungiyar Commonwealth na kare hakkin Bil Adama.”

Daga cikin masu ta’adi a kasar akwai ‘Yan Boko Haram, Makiyaya da sauran ‘yan ta’adda da ke yankin Arewa maso tsakiyar Najeriya kamar yadda ‘yan majalisar su ka ce.

Dazu kun ji cewa wasu miyagun ‘Yan bindiga sun sake yin ta’adi, inda su ka yi garkuwa da Bayin Allah a wasu garuruwan jihar Katsina, sun kuma raunata mutum guda.

Inda aka kai harin sun hada da karamar hukumar Faskari, Dandume da kuma Kankia.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng