Ba Kanal Baƙo kaɗai aka kashe ba: Dakarun soji sun nuna fushi kan ware sauran sojoji

Ba Kanal Baƙo kaɗai aka kashe ba: Dakarun soji sun nuna fushi kan ware sauran sojoji

- Dakarun soji sun nuna fushi kan wariya da aka nunawa sauran sojoji da suka mutu tare da Kanal Bako

- Kanal Bako ya kasance kwamandan sashi 2 na Operation Lafiya Dole, rundunar da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar

- Yan Boko Haram ne suka kashe kwamandan tare da wasu sojoji a harin bazata da suka kai masu

Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi fushi sosai da mahukunta kan rashin karrama sauran sojojin da yan Boko Haram suka kashe tare da kwamandansu, Kanal Dahiru Bako, Sahara Reporters ta ruwaito.

Kafin kisan nasa, Bako ya kasance kwamandan sashi 2 na Operation Lafiya Dole, rundunar da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.

Babban jami’in sojan ya rasa ransa a ranar Litinin, a wani harin bazata da yan ta’addan suka kai kansu, kamar yadda HumAngle ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Babban kwamandan Boko Haram da matansa 4 sun mika kansu ga sojoji a Borno

Ba Kanal Baƙo kaɗai aka kashe ba: Dakarun soji sun nuna fushi kan ware sauran sojoji
Ba Kanal Baƙo kaɗai aka kashe ba: Dakarun soji sun nuna fushi kan ware sauran sojoji Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sai dai an tattaro cewa ba a ambaci sauran sojoji uku da aka kashe tare da Bako ba balle a karrama su.

Sunayen sauran sojojin da aka kashe tare da kwamandan sune; Lance Corporal Oluwaseyi, Lance Corporal Nwobuji Desmond da Private Aliyu Ibrahim.

An ruwaito cewa babu wani sakon jaje daga hukumar sojin zuwa ga iyalan mamatan.

Wani makusanci, wanda ya zanta da HumAngle, ya bayyana cewa da hakan, hukumomin na ci gaba da nuna banbanci tsakanin wadanda ke karkashinsu da kuma gaza nuna jagoranci nagari.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: FG ta sanya jirgin shugaban ƙasa a kasuwa, za ta sayar da shi

A baya mun ji cewa, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya yi wa Rundunar Sojin Najeriya ta'aziyyar rasuwar Kanar Dahiru Bako da ya mutu sakamakon harin kwantan bauna da Boko Haram suka yi wa sojoji a Borno.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel