Wannan shine shan shayina na karshe a matsayin gwauro - Bashir Ahmad

Wannan shine shan shayina na karshe a matsayin gwauro - Bashir Ahmad

- Gobe Juma’a, 25 ga watan Satumba, Bashir Ahmad zai bar layin gwauraye

- Hadimin Shugaban kasar ya wallafa hotunansa a shafin Twitter yayinda yake shan shayin karshe a matsayinsa na gwauro

- Bashir dai zai auri sahibarsa Naema a babban masallacin Juma’a da ke GRA, Katsina

Kamar yadda kuka sani burin kowasu masoya da suka tsinci kansa a cikin shau’kin so, shine ganin sun mallaki junansu ta hanyar kulla aure a tsakaninsu.

Ko shakka babu hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya tsunduma sosai a cikin kaunar burin ransa, Naema.

Bashir ya nuna farin ciki a yayinda yake shirin fita daga sahun gwauraye, domin a gobe, Juma’a, 25 ga watan Satumba ne za a daura masa aure.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Likitoci sun kasa gano dalilin da ya sa ƴar shekara 15 ke kukan jini

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter mai ba Shugaban kasar shawara a shafukan zumunta, ya bayyana cewa a yau Alhamis, 24 ga watan Satumba, ya sha shayinsa na karshe a matsayin gwauro, inda ya jaddada cewa a gobe zai angwance.

Wannan shine shan shayina na karshe a matsayin gwauro - Bashir Ahmad
Wannan shine shan shayina na karshe a matsayin gwauro - Bashir Ahmad Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Ya wallafa hotunansa dauke da kofin shayi da ya hada domin yin karin kummalon safe, sai ya rubuta: “A zahiri wannan ya kasance kalaci na karshe da nayi a matsayin gwauro, matashi Bashir zai yi aure a gobe in sha Allah.”

A baya mun kawo maku cewa, Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a shafukan zumunta, na shirin angwancewa da masoyiyarsa.

Hadimin shugaban kasar zai auri amaryarsa, Naeemah Junaid a ranar Juma’a, 25 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: FG ta sanya jirgin shugaban ƙasa a kasuwa, za ta sayar da shi

Za a daura auren ne babban masallacin Juma’a na GRA da ke Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel