Barcelona ta yi wa Atletico Madrid gwanjon Luis Suarez a kan $7m

Barcelona ta yi wa Atletico Madrid gwanjon Luis Suarez a kan $7m

- ‘Dan wasa Luis Suarez ya bar Barcelona, ya koma Kungiyar Atleti Madrid

- ‘Dan kwallon mai shekara 33 ya bar Barcelona ne da kwallaye kusan 200

- A tarihin kungiyar, Suarez ne na biyu a wadanda su ka fi yawan kwallaye

Luis Suarez ya yi sallama da ‘yan wasan kungiyar Barcelona, sakamakon tsaida magana da kungiyar ta yi na saida shi zuwa Atletico Madrid.

Karshen zaman ‘dan wasan mai shekaru 33 a Barcelona ya kare, kungiyar ta saida ‘dan kwallon da aka sayo fam miliyan £75 a kan miliyan £5.5.

A zaman da ya yi na shekaru shida, Luis Suarez ya zurawa Barcelona kwallaye 198 a wasanni 283.

Jaridar Evening Standard ta bayyana cewa ‘dan wasan na kasar Uruguay ya bar filin wasan kungiyar ya na kuka saboda da ya yi da jama’a.

KU KARANTA: Bayan shekara da shekaru ana shari'a, Messi ya yi nasara a Kotu

Suarez ya na cikin ‘yan wasan da kungiyar ta saki a wannan watan. Sauran ‘yan kwallon da su ka bar Barcelona su ne: Ivan Rakitic, da Arturo Vidal.

Haka zalika Nelson Semedo da Arthur Melo duk sun tashi bayan zuwan sabon koci Ronald Koeman.

Ivan Rakitic ya koma kungiyar Sevilla da ya baro, yayin da Inter Milan ta saye Arturo Vidal. Semedo da Melo sun koma Wolves da kungiyar Juventus.

Barcelona ta tabbatar da tashin Luis Suarez a shafinta na yanar gizo, ta ce ta cin ma yarjejeniya da kungiyar Sifen, Atletico Madrid a kan ‘dan wasan gaban.

KU KARANTA: Messi bai samu wuri a sahun ‘Yan kwallon bana ba - UEFA

Barcelona ta yi wa Atletico Madrid gwanjon Luis Suarez a kan $7m
Luis Suarez celebrates Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Suarez ya koma kungiyar abokan gaban Barcelona ne bayan rade-radi sun yi karfi cewa kungiyar Juventus ta na sha’awar sayen tsohon ‘dan wasan na Liverpool.

Rahotanni sun ce lamarin komawarsa Italiya ya tabarbare ne a dalilin wahalar da aka fuskanta wajen yi masa takardun samun damar komawa aiki a Turin.

A jiya mun kawo maku rahoto cewa Lionel Messi ya fusata da labarin tashin Suarez bayan ana jita-jitar zai koma taka leda a kungiyar aokan gaba a Madrid.

Haka kuma Luka Jovic, mai bugawa gaban Real Madrid, ya bukaci a ba shi dama ya tashi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel