Yunƙurin fatattakar Oshiomhole daga APC: Jigon PDP ya roƙi APC ta ɗaga mashi ƙafa
- Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Ribas, Felix Obuah, ya bukaci mutanen jihar Edo da su yafe wa Oshiomhole
- Dan takarar jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu, ya sha kaye a hannun gwamna mai ci, Godwin Obaseki a zaben ranar Asabar, 19 ga watan Satumba
- Obuah ya bayyana cewa karar Oshiomhole daga APC na iya zama karshen siyasarsa a jihar
Biyo bayan mummunan kaye da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sha a zaben gwamnan jihar Edo, wani jigon PDP a jihar Ribas, Felix Obuah, ya rokin jam’iyyar da ta yafe wa Adams Oshiomhole.
Legit.ng ta ruwaito cewa wasu mambobin jam’iyyar sun yi barazanar korar Oshiomhole, wanda shine tsohon shugaban APC na kasa, daga jam’iyyar kan sakamakon zaben.
A martaninsa, Obuah ya roki APC a Edo da ta yafe wa Oshiomhole sannan ta dakatar da shirin korarsa daga jam’iyyar.
KU KARANTA KUMA: Da duminsa: FG da NLC za su gana ranar Alhamis kan karin kudin man fetur da lantarki
Obuah ya yi rokon ne cikin wani jawabi dauke da sa hannun mai bashi shawara na musamman a kokafin watsa labarai, Jerry Needam, a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba, a Port Harcourt.
Ya ce akwai bukatar yin wannan kiran domin neman a kori Oshiomhole ya samu goyon bayan mutane da yawa.
Jawabin ya zo kamar haka:
“Kamar yadda yake a zahirin gaskiya, ya nuna cewa APC ta fadi zaben gwamnan Edo ne saboda kafiya da girman kan Oshiomhole, dakatar dashi a wannan lokaci na iya kawo karshen dan siyasan wanda yake haifaffan Edo.
KU KARANTA KUMA: Gwamnati ta fitar da $1.96bn don ginin layin dogo daga Kano zuwa Jamhuriyar Nijar
“A matsayina na jigon kasa kuma dan siyasa tsantsa, ina iya hango tarin nadama da bakin ciki da ke yawo a zuciyar Oshiomhole, don haka a yafe masa.”
Obuah ya kuma bayyana cewa a matsayinsa na jigon PDP na jiha kuma wanda ya fahimci matsalolin siyasa, rasa kujerar shugabancin APC na kasa da yayi, da kuma rasa matsayinsa na ‘uba a siyasar Edo’ sun isa hukunci ga Oshiomhole.
“Ina mai jaje ya magoya bayan APC a Edo kan wahalar da suka sha a hannun Oshiomhole a matsayin gwamnan jihar Edo da kuma shugaban Jam’iyyar na kasa.
“Duk da haka, Ina rokonku da ku yafe masa amma idan sabanin rokona ya kasance, kuka yanke shawarar yasar dashi, Ina ganin PDP ba za ta karbe shi ba a cikin jam’iyyarmu mai mutunci da hadin kai."
A gefe guda, zaben kujerar gwamnan jihar Edo ya zo kuma ya tafi amma har yanzu akwai sauran barbashin kura tsakanin yan siyasa da masu sharhi kan lamuran yau da kullum.
Duk da cewa jam'iyyun siyasa 14 sukayi takara a zaben, sakamakon ya nuna cewa takaran na tsakanin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da All Progressives Congress APC.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng