UN: Ogunbiyi za ta yi aiki da Shugaban kamfanin CoP, Alok Sharma a Ingila
- Damilola Ogunbiyi ta samu babban mukami da majalisar dinkin Duniya
- Ogunbiyi ta na cikin wadanda za su shugabanci aikin fasaha a kasar Ingila
- Kafin nan ta yi aiki a Najeriya a matsayin Mai ba shugaban kasa shawara
Mun samu labarin farin ciki na wata Baiwar Allah daga Najeriya da ta samu babban matsayi a kasar Birtaniya.
Damilola Ogunbiyi ta samu shiga a gwamnatin Ingila, inda aka nada ta a wani kwamitin majalisar dinkin Duniya.
Ogunbiyi za ta rike kujerar shugabar kwamitin kula da taron da za ayi a kan sauyin yanayi a majalisar UN.
Wannan ‘yar Najeriya za ta yi aiki ne da shugaban kamfanin CoP na Ingila, Alok Sharma.
KU KARANTA: Ogunbiyi ta zama shugabar SEAforALL a UN
Jaridar Premium Times ta bayyana haka a wani rahoto da ta fitar a ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, 2020.
A daidai wanan rana ne kuma Damilola Ogunbiyi ta zauna da shugabannin Duniya game da harkar karfin wuta.
Misis Damilola Ogunbiyi ta na kokarin ganin an rage fitar da hayaki mai illa a wajen kona mai.
Makasudin zaman Damilola Ogunbiyi da shugabannin kasashen shi ne cin ma wannan buri nan da shekaru goma.
KU KARANTA: Hanyar da za a bi domin samun kudin tallafin Gwamnati na COVID-19
Wani jawabi da gwamnatin Birtaniya ta fitar ya tabbatar da shirin tsohuwar hadimin shugaban Najeriyar.
Yunkurin rage fitar da sinadarin ‘Carbon’ zai taimakawa sauran kasashen Duniya inji gwamnatin Birtaniyar.
Idan za ku tuna, Ministan wuta, Sale Mamman ne ya dakatar da Ogunbiyi daga aiki saboda wasu zargi a 2019.
Daga baya shugaba Muhammadu Buhari ya janye dakatarwar, wanda hakan ya ba ta dama ta yi murabus da kanta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng