APC ta yi rashi: Kotun zaɓe ta soke nasarar dan majalisar tarayya, ta buƙaci sabon zabe

APC ta yi rashi: Kotun zaɓe ta soke nasarar dan majalisar tarayya, ta buƙaci sabon zabe

- Jam’iyyar APC ta sake rasa wani kujera a majalisar wakilai ta tarayya

- Kotun zabe ta tsige dan takarar APC, Kasim Danjuma, kan zargin mallakar takardar shaidar kammala makaranta na jabu

- An tattaro cewa Danjuma ya gabatarwa da hukumar INEC takardar satifiket na jabu kafin zabe

Kasa da sa’o’i saba’in bayan ta sha kaye a zaben gwamnan Edo, kotun zaben majalisar dokokin tarayya da ke zama a Neja ta tsige Kasim Danjuma, dan takarar All Progressives Congress (APC) a zaben cike gurbi na mazabar Magama/Rijau da aka gudanar a jihar.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar da Danjuma a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi wanda aka gudanar a ranar 27 ga watan Maris, 2020.

Legit.ng ta tattaro cewa dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben cike gurbin, Emma Alamu, ya tunkari kotun zabe kan zaben.

KU KARANTA KUMA: Jonathan, Sambo da wasu manyan yan Najeriya sun ziyarci fadar marigayi Sarkin Zazzau

APC ta yi rashi: Kotun zaɓe ta soke nasarar dan majalisar tarayya, ta buƙaci sabon zabe
APC ta yi rashi: Kotun zaɓe ta soke nasarar dan majalisar tarayya, ta buƙaci sabon zabe Hoto: House of Reps NGR.
Source: Twitter

Ya zargi Danjuma da gabatar da takardun bogi ga hukumar INEC wanda hakan ne ya bashi damar takara a zaben cike gurbin.

Alamu ya bayyana cewa Danjuma ya gabatar da takardar kammala makarantar Firamare na bogi sannan ya yi takardar haihuwa na jabu domin INEC ta tantance shi.

Mohammed Ndayako, lauyan mai kara, ya bukaci kotun zaben da ta soke nasarar dan takarar na jam’iyyar APC.

Ndayako ya kuma bukaci kotun ta gabatar da wanda yake karewa a matsayin wanda ya lashe zaben.

Don haka kwamitin mutum uku na kotun zaben karkashin jagorancin Justis B. F. Zubairu, ya saurari karar sannan ya soke nasarar Danjuma.

Kotun zaben ya ce mai karar ya gabatar da hujja mai karfi cewa wanda ake karar ya gabatar da takardun bogi ga INEC wanda ya bashi damar takara a zaben.

KU KARANTA KUMA: Wadatar da kasa da abinci: Buhari ya zabtare farashin taki a Nigeria

Don haka, ya soke zaben sannan ya umurci INEC ta gabatar da sabon zabe a mazabar cikin kwanaki 90 masu zuwa.

A baya mun ji cewa kotun daukaka karar zaben gwamnan jihar Kogi da ke zamanta a Abuja, ta yi fatali da kararraki hudu da ke kalubalantar zaben Gwamna Yahaya Bello.

Kotun a yayin zamanta da ta gudanar a ranar Asabar cikin birnin Abuja, ya tabbatar da nasarar Yahaya Bello a matsayin zababben gwamnanjihar Kogi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel