Luka Jovic ya na so ya koma Jamus, Luiz Suarez ya yarda ya koma Atletico

Luka Jovic ya na so ya koma Jamus, Luiz Suarez ya yarda ya koma Atletico

- Dan wasan gaban Real Madrid, Luka Jovic ya bukaci a ba shi dama ya tashi

- Luka Jovic mai shekara 22 ya ki yin abin kwarai bayan an saye shi kan €60m

- Luis Suarez ya amince ya koma Atletico Madrid ne bayan zuwan sabon Koci

‘Dan wasan kasar Serbia, Luka Jovic ya rubuta takarda ya na neman tashi daga kungiyar Real Madrid bayan shekara guda rak da zuwansa kulob din.

Rahotanni sun bayyana cewa Luka Jovic ya roki Real Madrid ta ba shi damar komawa kungiyar Eintracht Frankfurt da ya baro a shekarar da ta gabata.

‘Dan kwallon mai shekara 22 ya gaza samun wuri a Real Madrid bayan ya ci kwallaye biyu a bara. Jovic ya bugawa Zinedine Zidane wasanni 27 ne a bara.

KU KARANTA: Kocin Barcelona zai tafi kotu saboda sallamarsa da aka yi

Jovic ya zo Santiago Bernabeu ne bayan an kashe kusan fam miliyan €60 wajen sayo shi.

Jaridar Sun Sport ta ce ‘dan wasan gaban ya gagara burge Mai horas da Real Madrid Zinedine Zidane, Wasanni hudu kadai aka take da Jovic a La-liga.

A gefe guda kuma, Luis Suarez ya yarda ya koma Atletico Madrid bayan Barcelona ta soke kwantiragin ‘dan wasan gaban mai shekaru 33 a Dniya.

Shahararren ‘dan jaridar nan, Fabrizio Romano, ya ce ‘dan wasan na Uruguay ya zabi Atlético.

Luka Jovic ya na so ya koma Jamus, Luiz Suarez ya yarda ya koma Atletico
Watakila Luka Jovic ya bar Madrid
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Bale zai koma kungiyar da ya baro bayan shekaru 7 a Madrid

A cewar jaridar Mundo Deportivo Suarez ya zauna da Miguel Angel Gil Marin da Diego Simeone, zai sa hannu a kwangilar shekaru biyu da kungiyar ta Madrid.

Mai horas da kungiyar Atletico Madrid, Diego Simeone ya tabbatarwa tsohon ‘dan wasan na Ajax da Liverpool cewa zai yi da shi bayan zuwansa Juventus ya faskara.

A makon nan kuma kun ji cewa Kungiyar Liverpool ta kasar Ingila ta gyara tsakiyarta bayan ta saye Thiago Alcantara, daga kungiyar Bayern Munich a kan kudi $26m.

‘Dan wasan mai shekaru 29 ya yi shekara bakwai a Bayern Munich bayan ya bar Barcelona.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel