Labaran Duniya: N’Daou zai rike Mali kafin ayi zaben sabon Shugaban kasa
- Sojojin Tawaye sun sanar da sabon shugaban rikon-kwarya a kasar Mali
- Ba N’Daou zai rike kasar Mali har zuwa lokacin da za ayi babban zabe
- N’Daou tsohon Kanal ne mai shekaru 70, kuma ya taba yin Ministan tsaro
Tsohon Ministan tsaron kasar Mali, Ba N’Daou, sojojin tawaye su ka sanar a matsayin sabon shugaban gwamnati na rikon kwarya.
Shugaban sojojin tawayen Mali ya bada wannan sanarwa a ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, 2020.
Kamar yadda sojoji su ka bayyana, Ba N’Daou zai rike kasar Mali na wucin-gadi, har zuwa lokacin da za ayi zabe domin tsaida shugaban kasa.
Kungiyar kasashen Afrika ta AU ta yi kira ga sojojin da su ka yi juyin-mulki a kasar Mali, su yi maza su mikawa farar hula mulkin kasar.
KU KARANTA: Jonathan zai jagoranci shugabannin Afrika zuwa Mali
Wannan gwamnati ta rikon kwarya za ta yi shekara guda da rabi ta na jan ragamar kasar, har a shirya sabon zabe, a fito da shugaban kasa.
Kwanan nan shugaban sojojin tawaye, Kanal Assimi Goita ya gana da shugabannin Afrika domin cin ma matsaya game da makomar kasar.
ECOWAS ta bukaci sojoji su mikawa farar hula mulki a Mali, kungiyar ta ce sai an yi haka ne za ta cire takunkumin da ta makawa kasar.
Kwanan baya sojoji su ka hambarar da gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita. An yi hakan ne bayan tsawon lokaci ana ta rikicin siyasa.
KU KARANTA: Shugaban Mali ya yi murabus saboda a zauna lafiya
Ita ma kungiyar AU ta bukaci sojoji su fito da shugaba Ibrahim Keita, Firayim Minista, Boubou Cisse, da duk manyan gwamnati da aka tsare.
Mai magana da yawun bakin sojojin da su ka yi juyin-mulki, Kanal Ismael Wague ya shaidawa ‘yan jarida cewa an huro masu wuta su bada mulki.
Ismael Wague ya ce kasar na iya fuskantar cikakkiyar takunkumi muddin ba su nada shugaban rikon kwarya na farar hula ba, abin da ba su so ba.
Bayan juyin-mulkin da aka yi, kun ji cewa gwamnatin Najeriya da kungiyar ECOWAS sun Allah-wadai da hambarar da Gwamnatin farar hula a kasar Mali.
Amurka da Faransa duk sun yi tir da yadda aka yi amfani da soji wajen kifar da gwamnati.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng