Jonathan, Sambo da wasu manyan yan Najeriya sun ziyarci fadar marigayi Sarkin Zazzau

Jonathan, Sambo da wasu manyan yan Najeriya sun ziyarci fadar marigayi Sarkin Zazzau

- Manyan shugabannin Najeriya na ci gaba da ta’aziyyar marigayi Sarkin Zazzau

- A ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba ne aka yi rashi na babban basakare a jihar Kaduna, Sarki Shehu Idris, ya mutu yana da shekaru 84 a duniya

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr Goodluck Jonathan, ya jagoranci wata tawaga zuwa fadar marigayi sarkin a ranar Talata, 22 ga watan Satumba

A safiyar yau Talata, tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr Goodluck Jonathan, ya jagoranci wata tawaga zuwa jihar Kaduna domin yin ta’aziyyar marigayi sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, yana da shekaru 84.

Dr Jonathan wanda ya samu rakiyan tsohon mataimakin Shugaban kasa, Architect Namadi Sambo, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, Sanata Jeremiah Useni da kuma tsohon gwamnan jihar Adamawa, Boni Haruna.

KU KARANTA KUMA: Yadda dan majalisa ya shiga daji da kansa ya ceto yan mazabarsa da yan bindiga suka sace a Kwara

Da yake alhinin marigayin, Jonathan ya rubuta a Twitter:

“A yau, mun je Zaria domin ta’aziyya ga gwamnatin jihar Kaduna, masarautar Zazzau da iyalan marigayi sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.

“Marigayi basaraken wanda ya shafe kusan rabin karni kan mulki ya bar tarihi ta bangaren gina zaman lafiya, kuma a matsayin mutum da ya kare martabar al’adun mutanensa. Allah ya saka masa da Jannatul Firdaus.”

A nashi bangaren, Gwamna Matawalle ya ce:

“Marigayi sarkin Zazzau ya yi rayuwa mai aminci inda ya yarda da hadin kai, burina ne ganin yan bayan masu tasowa sun yi koyi da irin rayuwar da yayi.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu yana cikinmu: APC ta ƙaryata jita jitar fatattakar Oshiomole daga jam'iyyar kwata kwata

Jonathan, Sambo da wasu manyan yan Najeriya sun ziyarci fadar marigayi Sarkin Zazzau
Jonathan, Sambo da wasu manyan yan Najeriya sun ziyarci fadar marigayi Sarkin Zazzau Hoto: @GovKaduna
Asali: Facebook

A gefe guda, mun ji cewa cikin mutane biyu za'a zabi sabon sarki; daya na kusa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kuma abokin gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Na farko, Alhaji Munir Ja'afari, mai shekaru 66, babban dan kasuwa kuma tsohon shugaban hukumar NIMASA.

Sai Alhaji Ja'afaru Nuhu Bamalli, tsohon jakadan Najeriya zuwa kasar Thailand.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel