Godwin Obaseki ya shiga sahun Gwamnonin da su ka zarce bayan sun sauya-sheka

Godwin Obaseki ya shiga sahun Gwamnonin da su ka zarce bayan sun sauya-sheka

- Godwin Obaseki ya kafa tarihin lashe zabe biyu a jere a Jam’iyyu dabam-bam

- Gwamnan na Edo ya shiga sahun Aminu Waziri Tambuwal da Samuel Ortom

- A baya an samu Gwamnonin jihohin da su ka sha kashi bayan sun sauya-sheka

Mai girma Godwin Obaseki na jihar Edo ya yi nasarar sake lashe zaben 2020, wannan karo a karkashin PDP da yi tika da kasa a shekaru hudu da su ka wuce.

Da wannan nasara, Godwin Obaseki ya zama gwamna na uku daga 2015 da ya lashe zaben gwamna sau biyu a jere, ya yi hakan ne a mabanbatan jam’iyyu.

Legit.ng Hausa ta kawo maku tarihin wadanda su ka yi irin wannan dace a tarihin siyasar Najeriya

KU KARANTA: Siyasa babu gaba: APC ta taya PDP murnar lashe zabe a Edo

Samuel Ortom

A 2015 Samuel Ortom ya lashe zaben Gwamnan Benuwe a karkashin jam’iyyar APC. Bayan shekaru uku, ya sauya sheka zuwa jam’iyyarsa ta asali ta PDP, ya kuma zarce a kan mulki.

Gwamna Ortom ya doke Emmanuel Jime na APC bayan zaben ya kai zuwa ga zagaye na biyu.

Aminu Waziri Tambuwal

Wani gwamnan ya ke cikin irin wannan littafin tarihi shi ne Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal. Tsohon shugaban majalisar ya fice daga APC da ta ba shi nasara a 2015, ya zarce a karkashin PDP.

Aminu Waziri Tambuwal ya lashe zaben 2019 ne da kuri’a 342 bayan wanki hula ya kai shi dare.

Wani Gwamna a wannan sahun shi ne Isa Yuguda wanda ya zama gwamnan Bauchi a karkashin jam’iyyar ANPP, daga baya ya sauya-sheka zuwa PDP, ya kuma yi nasara a zaben 2011.

KU KARANTA: APC ta na zargin Fayemi ya marawa Obaseki baya a zaben Jihar Edo

Godwin Obaseki ya shiga sahun Gwamnonin da su ka zarce bayan sun sauya-sheka
Gwamna Godwin Obaseki, Shuaibu da Wike
Asali: UGC

Sauran wadanda su ka yi irin wannan yunkuri, amma su ka sha kashi su ne Abubakar Rimi a 1983 bayan ya bar jam’iyyar PRP zuwa NPN. Sabo Bakin-Zuwo ya doke shi a jihar Kano.

A 2003, tsohon gwamnan jihar Borno, Abubakar Mala Kachalla ya bar ANPP zuwa AD.A karshe ya sha kashi a hannun Sanata Ali Modu Sheriff wanda ya yi takara a tsohuwar jam’iyyarsa.

Haka zalika Mahmud Shinkafi ya gaza zarcewa a jihar Zamfara a 2011 bayan ya koma PDP daga ANPP.

A makon nan kun ji labarin ‘dan-gashin Osagie Ize Iyamu wanda ya sha kashi a zaben gwamnan jihar Edo a 2016 da 2020. Ize Iyamu ya jarraba sa’arsa a APC da PDP, amma bai dace ba.

Obaseki ne ya doke Osagie Ize-Iyamu sau biyu a jere, a duk zabukan ya lashe kananan hukumomi 13.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng