Mijina yana amfani da dadironsa domin ci mun mutunci - Matar aure ta kokawa kotu

Mijina yana amfani da dadironsa domin ci mun mutunci - Matar aure ta kokawa kotu

- Wata mata, Kudrat Oyewole, a ranar Talata, ta bukaci kotu ta raba aurenta da mijinta Sikiru, saboda gaza sauke nauyin aure da kuma cin zarafinta da ya ke yi

- Kudrat ta shaidawa kotun cewa, Sikiru na daukar bidiyo a wayarsa, na yadda yake saduwa da dadironsa, yana kunnawa a gaban ta, don ya kuntata ma ta

- Sai dai a nashi bangaren, Sakiru, ya karyata zargin Kudrat, yana mai cewa matar tasa ta na da dabi'ar yin yaji zuwa gidansu da zaran sun samu dan sabani

Wata mai dinki, Kudrat Oyewole a ranar Talata, ta kai karar mijinta Sikuru, gaban kotun zamantakewar aure da ke Ile-Tuntun, jihar Ibadan.

Ta bukaci kotun da ta warware auren nasu, da suka yi shekaru biyu da suka wuce.

Kudrat na neman mijin ya sake ta ne akan cin zarafin da ya ke yi mata, da kuma gaza sauke nauyin aure da ya rataya a wuyansa.

Matar, mai yaro daya, ta shaidawa mai shari'a Henry Agbaje, shugaban kotun, cewar ta jure bakin ciki da azaba a gidan aurenta, sai dai yanzu ba za ta iya ci gaba da haka ba.

KARANTA WANNAN: Daukar mutane 774,000 aiki daga jihohi 36: Muhimmin bayani daga FG

Mijina yana amfani da dadironsa domin ci mun mutunci - Matar aure ta kokawa kotu
Mijina yana amfani da dadironsa domin ci mun mutunci - Matar aure ta kokawa kotu
Source: Twitter

Ta kara da cewa mijinta na kaurace mata da yaronta, yana zuwa yana yin rayuwar sa ba tare da waiwayar inda suke ko sanin halin da suke ciki ba.

"Sikiru ya ci gaba da bijirewa rokona, na tallafawa kasuwanci na, ya rika biyan kudin hayar shagon da nake sana'a a ciki.

"Kuma ya shaida mun cewa ina da zabin ficewa daga gidansa idan har na gaji da zama da shi a halin da ya ke ciki yanzu ba.

"Har ta kai, Sikiru, na nadar sauti da bidiyo a wayarsa, na yadda yake saduwa da matan da yake zaman dadiro da su, yana kunnawa a gabana, don ya kuntata mun.

"Na kai kararsa ga iyayensa, amma babu wani abu da ya canja.

"Makonni biyu da suka wuce lokacin da na kaiwa dan uwana ziyara, ya canja kwadon gidan, ya hana ni shiga, saboda ban dawo akan lokaci ba.

"Ni na gaji da zama da Sikiru, ina son nima na samu ci gaba a rayuwata," Kudrat ta shaidawa kotun.

KARANTA WANNAN: Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya aike da sako ga Tinubu, Oshiomhole da ire irensu

Sai dai da ya ke mayar da bayani, Sikiru, wanda ke zaune a yankin Fatusi, Ibadan, ya karyata wannan zargi da matar ta ke yi masa.

Ya shaidawa kotun cewa matarsa na da dabi'ar yin yaji duk lokacin da suka samu wata yar matsala, ko da ba ta zuwa gida bace, sai ta tafi.

"Kudrat ta je ta nemi aiki ba tare da sani ba kuma na shaida mata cewa irin wannan dabi'ar ba ya faruwa a cikin gidanmu.

"Wannan shine dalilin da ya sa na hanata shiga gidan a lokacin. Na yi iya bakin kokarina na biyan kudin hayar shagonta, amma ba ta da hakuri akan kokarin nawa," cewar Sikiru.

Da ya ke yanke hukunci, Agbaje ya roki ma'auratan da su kara hakuri da junansu.

Ya bukace su, da su gabatar da kwararan hujjoji gaban kotun, inda ya dage shari'ar har sai ranar 6 ga watan Oktoba domin sake yin wani zaman.

A wani labarin, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, da ire irensa, barazana ne ga demokaradiyyar Nigeria.

Obaseki ya bayyana hakan a ranar Talata a tattaunawa da shi cikin 'Shirin Safiya' na gidan talabijin din Arise TV, wata kafar watsa labarai ta jaridar THISDAY.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel