Zaben Edo: Obaseki ya sha alwashin gasa wa Oshiomhole aya a hannu

Zaben Edo: Obaseki ya sha alwashin gasa wa Oshiomhole aya a hannu

- Akwai yiwuwar barkewar sabon rikici tsakanin Godwin Obaseki da tsohon ubangidansa a siyasa, Adams Oshiomhole

- Obaseki ya sha alwashin cewa ba zai ji kan tsohon shugaban na APC ta kasa ba idan har ya ci gaba da “sakin zakunansa”

- Gwamnan na Edo ya yi nasarar zarcewa kan kujerarsa a ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, bayan ya lashe zabe a kananan hukumomi 13 cikin 18

Godwin Obaseki, zababben gwamnan Edo a karo na biyu, ya sha alwashin gasa wa tsohon ubangidansa, Adams Oshiomhole aya a hannu idan har ya ci gaba da “sakin zakunansa.”

A tuna cewa akwai gabar siyasa a tsakanin Obaseki da Oshiomhole tun a 2019.

Hakan ya sa gwamnan ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP) a watan Yunin 2020.

Obaseki, kafin sauya shekarsa zuwa jam’iyyar adawa, an hana mashi tikitin takara a karkashin inuwar APC saboda zargi da ke tattare da takardar shaidar karatunsa.

Lamari da wasu dama suka bayyana a matsayin makircin Oshiomhole.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Jama'ar Edo sun bai wa masu magudin zabe kunya - Kwankwaso

Zaben Edo: Obaseki ya ya alwashin gasa wa Oshiomhole aya a hannu
Zaben Edo: Obaseki ya ya alwashin gasa wa Oshiomhole aya a hannu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Bayan an sha gwagwarmaya na watanni, Gwamna Obaseki ya yi nasara yayinda ya kayar da Ize-Iyamu a zaben gwamna na ranar Asabar, 19 ga watan Satumba.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar da gwamnan na Edo a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya cike dukkanin ka’idoji da kuri’u 307,955 sannan ya kawo kananan hukumomi 13 cikin 18 a jihar Edo.

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan sun bayyana nasarar Obaseki a matsayin nasara ga damokradiyya.

Da yake magana a tashar Arise TV’ na safe a ranar Talata, 22 ga watan Satumba, Obaseki ya ce ba zai fatattaki Oshiomhole ba kamar yadda tsohon Shugaban na APC ya yi barazanar yi.

Sai dai Obaseki ya ce ba zai nuna jin kai ba idan Oshiomhole ya ci gaba da tayar da fitina ta hanyar sakin zakunansa.

KU KARANTA KUMA: Kabilar Jarawa: Jama'ar kasar India da masana'antar Bollywood bata bayyanawa

“Ba ni da niyan korar Oshiomhole daga Edo, amma idan ya ci gaba da sakin zakunansa, ba za mu sassauta masa ba,” in ji gwamnan.

A gefe guda, jam’iyyar APC ta fitar da jawabi bayan an sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Edo wanda aka gudanar a ranar 19 ga watan Satumba, 2020.

APC ta taya Gwamna Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP murnar lashe wannan gagarumin zabe.

Wannan jawabi ya fito ne daga bakin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar mai mulki, Alhaji Mai Mala Buni a ranar Litinin, 21 ga watan Satumba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel