Ku gurfanar da barayin man fetur - Wike ga jami'an tsaro

Ku gurfanar da barayin man fetur - Wike ga jami'an tsaro

- Dakarun Sojojin ruwa na jihar Ribas sun kaiwa Gwamnan jihar Rivers ziyara inda suka tattauna da shi

- Gwamna Wike ya samarwa sojojin ruwan, jiragen ruwa masu bindiga guda 5 saboda masu satar man fetur

- Gwamna Wike yace ya bunkasar da harkokin tsaro da asibitocin mata da yara da kuma tituna a jihar Ribas

Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers yayi kira ga cibiyoyin tsaro da su gurfanar da masu yiwa gwamnati zagon kasa ta hanyar satar man fetur a gabar kotu.

Wike yayi wannan maganar ne a ranar Litinin, lokacin da daliban kwalejin horar da sojin ruwa suka kai masa ziyara a gidan gwamnati na Fatakwal

A cewarsa, ya kamata a dakatar da satar man fetur don hakan yana zama zagon kasa ga cigaban kasa, Vanguard ta wallafa.

Gwamnan yace mulkinsa ya bai wa cibiyoyin tsaro taimako, musamman sojojin ruwa wurin basu jiragen ruwa na yaki guda 6 saboda tabbatar da tsaro a cikin ruwa.

"Zamu kara samar da jiragen ruwa masu bindiga ga sojojin ruwa saboda hana satar man fetur a jihar. Kada a siyasantar da harkar tsaro, ko kuma a danganta hakan da wata jiha," yace.

KU KARANTA: Zaben Edo: Obaseki ya magantu bayan lallasa Ize-Iyamu na APC da yayi

Ku gurfanar da barayin man fetur - Wike ga jami'an tsaro
Ku gurfanar da barayin man fetur - Wike ga jami'an tsaro. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamna Obaseki ya aike wa da Ize-Iyamu sako mai muhimmanci

A cewarsa, "Babu kasa ko kuma jiha da za ta ce bata da tsaro. A wannan jihar tamu, mun dage kwarai a harkar tsaro shiyasa rashin tsaro ya ragu kwarai."

"Irin kokarin da kake yi idan wani ya kawo ma kayanka farmaki, shi zakayi idan ka kama wani da laifi kai ma kayan gwamnati farmaki," cewar sa.

Ya yi kira ga wadanda suka kai mishi ziyara da suje su duba irin cigaban da aka samu a jihar Ribas.

"Muna gina tituna a wurare daban-daban. Ana dab da karasa asibitocin mata da yara. Sannan zamu bude makarantar kwallon kafa ta Real Madrid nan bada jimawa ba" a cewarsa.

A wani labari na daban, Gwamna Wike na jihar Ribas a daren Juma'a ya bayyana mamakinsa a kan tambayar da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, yayi masa.

Wike ya sanar da cewa babban dan sandan Najeriyan ya bukacesa da ya tattara komatsansa ya bar jihar Edo duk da yace ba a dauka wannan matakin a kan sauran gwamnonin APC da suka ziyarci jihar ba.

Gwamnan ya ce ya sanar da sifeta din 'yan sandan cewa, ya ziyarci jihar domin duba yadda zaben da za'ayi ranar Asabar zai tafi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel