Gwamnatin Katsina ta musanta bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje da shaguna
- Bayan caccakar da Gwamna Masari na jihar Katsina ya fara fuskanta, ya musanta alkawarin cewa zai gwangaje 'yan bindigar daji
- Kamar yadda sakataren yada labarai na gwamnan jihar Katsinan ya tabbatar, SSG da aka alakanta da zancen yace bai san komai a kai ba
- Dr. Mustapha Inuwa ya sanar da cewa, tallafin an tabbatar da cewa za a bai wa Fulani makiyaya ne ba tubabbun 'yan bindiga ba
Gwamnatin jihar Katsina ta musanta yi wa tubabbun 'yan bindiga alkawarin basu gidaje da shagunan kasuwa.
A wata takardar da daraktan yada labarai na Gwamna Aminu Belllo Masari, Abdu Labaran Malumfashi ya fitar, ya ce sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dr Mustapha Inuwa, wanda aka alakanta da labarin bai san komai a kai ba.
Jaridar Daily Trust ta tunatar cewa, cece-kucen ya fara ne tun bayan wani zama a satin da ya wuce inda SSG yake amsa wata tambaya akan ko gwamna zai sa makiyaya a cikin tsarinshi na taimako.
"Muna so mu taimaki mata musamman wadanda aka kashe wa mazaje. Amma zamuyi hakan ne idan zaman lafiya ya wanzu," a cewar SSG.
SSG yace, Akwai yan Fulani da dama da suke zaune a cikin daji a mawuyacin yanayi kuma bazasu iya shigowa cikin mutane ba saboda yadda ake daukansu a matsayin barayi.
Ya kara da cewa ,hakika gwamnati tana da niyyar canja tsarin gidajensu na daji kuma su taimaki wadanda ke da niyyar barin dajin.
A cewar Dr Inuwa, bayan Runka,tsarin zai biyo ta Yantumaki daganan sai dajin tsakanin Yantumaki da Maidabino don samar wa Fulani matsuguni.
Yace za'a gina asibitoci da kasuwanni a wuraren kuma za'a samar da filayen gina gaidaje da gonaki.
Yace tsarin zai dakatar da yan bindiga daga shigowa wurare kamar Zakka, Dutsinma da kuma Yantumaki, Matazu, Musawa da sauran wurare.
KU KARANTA: Zaben Edo: Buhari bai taba amfani da karfin ikonsa wurin magudi ba - El-Rufai
KU KARANTA: Hotuna: Dubban mazauna Edo sun sha shagali bayan Obaseki ya fito murna a tituna
A wani labari na daban, tsohon dan majalisar dattawa wanda ya wakilci jihar Kaduna ta tsakiya a majalisa karo ta takwas, Sanata Shehu Sani, ya caccaki Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a kan yunkurin gwangwaje tubabbun 'yan bindiga da gonaki da gidaje.
A yayin martani ta shafinsa na Twitter, Sanata Sani, ya ce wannan kawai hanya ce ta gwangwaje masu laifi.
Kamar yadda yace, wannan karamcin zai kara fadada laifuka tare da kara bai wa wasu kwarin guiwa.
"Gwamnatin jihar Katsina tana kokarin bai wa 'yan bindiga gonaki, shagunan kasuwa da gidaje wanda hakan hanya ce ta karrama 'yan ta'adda.
"Hakan kuwa zai kara musu kardin guiwa tare da bai wa wasu sha'awar shiga harkar. Zai kara tsananta matsalar tsaro a yankin arewa," Sani ya wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng