‘Ya ‘yan Jam’iyya a Ekiti sun ce Gwamna Fayemi ya goyi bayan takarar Obaseki

‘Ya ‘yan Jam’iyya a Ekiti sun ce Gwamna Fayemi ya goyi bayan takarar Obaseki

- Wasu ‘Ya ‘yan APC sun zargi Gwamnan Ekiti da ba PDP goyon baya a Edo

- ‘Yan Jam’iyyar sun ce Kayode Fayemi ya marawa Godwin Obaseki baya

- Godwin Obaseki ya doke ‘Dan takarar APC Osagie Ize-Iyamu a zaben jihar

Wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki a jihar Ekiti, su na ikirarin gwamna Kayode Fayemi ya na neman korarsu daga jam’iyya.

Jaridar Premium Times ta ce wadannan ‘ya ‘yan jam’iyya da su ke samun sabani da gwamnan Ekiti, sun jefe shi da zargin aikata zagon-kasa.

A cewarsu, Dr. Kayode Fayemi ya goyi bayan ‘dan takarar jam’iyyar PDP, Godwin Obaseki, a zaben gwamnan jihar Edo da aka yi kwanan nan.

Gwamna mai-ci Godwin Obaseki ne ya yi galaba a kan Osagie Ize-Iyamu da jam’iyyarsa ta APC.

KU KARANTA: Edo: Buhari ya yi wata ganawa da Ganduje da Mai Mala Buni

Godwin Obaseki ya koma jam’iyyar PDP ne sakamakon hana shi takara a jam’iyyar APC, bayan ya sauya-sheka, ya yi galaba kan Fasto Osagie Ize-Iyamu.

‘Ya ‘yan jam’iyyar da ake rikici da su sun bayyana cewa gwamna Fayemi ne ya ke da hannu a yunkurin da ake yi na fatattakar su daga jam’iyyar APC.

Bayan haka sun ce gwamnan ya yi ruwa da tsaki wajen ganin takwaransa, Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP ya doke ‘dan takarar APC domin koma kan mulki.

A wata takarda da Bamgboye Adegoroye ya aikawa jaridar Premium Times a ranar 21 ga watan Satumba, 2020, ya zargi Fayemi da yi wa APC makarkashiya.

KU KARANTA: Ize Iyamu: ‘Dan siyasar da ya sha kashi a PDP, ya koma APC, ya sake shan kashi

‘Ya ‘yan Jam’iyya a Ekiti sun ce Gwamna Fayemi ya goyi bayan takarar Obaseki
Gwamna Kayode Fayemi wajen kamfe
Asali: Facebook

Adegoroyo ya ce: “Wani lamari ya na aukuwa a reshen jam’iyyarmu ta APC ta jihar Ekiti. Gwamnanmu kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Dr Kayode Fayemi, ya na neman korar shugabannin jam’iyya, bayan ya fito ya yi wa jam’iyya zagon-kasa, ya daura gwamnan jihar Edo.”

Mista Bamgboye Adegoroye ya ce gwamnan na amfani da wani Ajigbolamu wajen cin ma manufarsa. A cewarsa, wannan mutumi bai dade da barin PDP ba.

A jihar Ekiti an dade ana samun baraka a jam’iyyar APC. A makon da ya gabata ne ku ka ji cewa ana shirin dakatar da wasu manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar fiye da 10.

Daga cikin wadanda za a ladabtar har da hadimin shugaba Muhammadu Buhari, Babafemi Ojudu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng