Yanzu nan: Buhari, Ganduje da Buni sun hadu a fadar Shugaban kasa

Yanzu nan: Buhari, Ganduje da Buni sun hadu a fadar Shugaban kasa

- Gwamna Dr. Abdullahi Ganduje da Mai Mala Buni sun ziyarci Aso Villa

- Shugaban kasar ya karbi bakuncin jagorarin APC ne bayan zaben Edo

- Jam’iyyar APC ta sha kashi a hannun PDP a zaben Gwamnan da aka yi

A yau ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, 2020, Shugaba Muhammadu Buhari ya hadu da Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Mai Mala Buni.

Ganawar shugaban kasar da shugaban rikon kwaryar jam’iyyar APC da gwamnan Kano ta na zuwa ne jim kadan da kammala zaben gwamnan Edo.

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje shi ne shugaban yakin neman zaben jam’iyyar APC a zaben da PDP ta yi nasarar lashewa a jihar Edo.

KU KARANTA: Edo: Abin da ake fadawa Oshiomhole da Tinubu game da nasarar PDP

‘Yan jarida sun tabbatar da cewa shugaban kasar ya sa labule da Abdullahi Ganduje da Mai Mala Buni ba tare da sun yi wa kowa magana a fadar ba.

Ana zargin dalilin ganawar shugaban kasar da wadannan gwamnoni bai rasa nasaba da zaben Edo.

Idan za ku tuna, Fasto Osagie Ize-Iyamu wanda jam’iyyar APC ta tsaida takara ya sha kashi ne a hannun gwamna mai-ci, Godwin Obaseki na PDP.

Abdullahi Ganduje da Takwaransa na jihar Imo, Gwamna Hope Uzodinma su na tare a garin Benin inda su ke yi wa jam’iyyar APC yakin neman zabe.

KU KARANTA: Ize Iyamu: ‘Dan siyasar da ya sha kashi a PDP da APC

Sanata Hope Uzodinma ya na cikin kwamtin gwamna Abdullahi Ganduje na yakin neman zabe.

Bayan tattaunawar da aka yi a ofishin shugaban kasar, an hangi Mai girma Abdullahi Ganduje da Mai Mala Buni su na kauracewa tambayoyin ‘yan jarida.

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi magana game da zaben jihar Edo, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ba ya amfani da karfinsa wajen murde zabe.

Ganin Obaseki ya yi nasara da kuri'u 307,955 a zaben, El-Rufai ya ce ya dauka APC za ta ci zabe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel