El-Rufa'i ya ware ranar hutu a Kaduna don yi wa marigayi sarkin Zazzau addu'o'i

El-Rufa'i ya ware ranar hutu a Kaduna don yi wa marigayi sarkin Zazzau addu'o'i

- A ranar 20 ga watan Satumba ne mutanen Zazzau su ka wayi gari da labarin babban rashi

- Mai Martaba Shehu Idris, sarkin Zazzau na 60, ya rasu a wani asibitin sojoji da ke garin Kaduna

- Marigayi sarki Shehu ya fi kowanne sarki a tarihin masarautar Zazzau dadewa a kan karagar mulki bayan ya shafe sheakaru 45 yana sarauta

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta ware kwanaki uku domin alhinin mutuwar marigayi sarkin Zazzau, Shehu Idris.

Muyiwa Adekeye, mai bawa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, shawara a harkar kafafen sadarwa ya fitar da sanarwa dangane da hakan.

A cikin sanarwar, wacce ta fito ranar Litinin, Mista Adekeye ya ce; "Za a bude ofisoshi a ranakun 21 da 22 ga watan Satumba, 2020.

"Akwai hutun aiki a ranar 23 ga watan Satumba domin karrama shi."

Sanarwar ta kara da cewa za a saukar da tutar Najeriya zuwa tsakiyar sandar karfe na tsawon kwanakin alhinin mutuwar Sarkin.

KARANTA: Makusanta shugaban kasa su na amfani da biyan tallafin man fetur don azurta kansu - Shugaban NNPC

A ranar Lahadi, 20 ga Satumba, marigayi sarkin Zazzau ya rasu a wani asibitin sojoji da ke Kaduna bayan gajeriyar jinya.

Masana tarihi sun ce Gunguma wani daga cikin jikokin Bayajidda ne ya fara rike sarautar kasar Zazzau. A tarihi an yi sarakunan Habe 60 zuwa Marigayi Shehu Idris.

El-Rufa'i ya ware ranar hutu a jihar Kaduna domin yi wa marigayi sarkin Zazzau addu'o'i
Marigayi sarkin Zazzau Shehu Idris
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta zakulo jerin wadanda aka tunanin za su iya samun gadon wannan kujera. Kafin nan ya kamata a san cewa akwai gidajen sarauta daban-dabam a kasar Zariya; Gidan Mallawa, Gidan Barebari, da Gidan Katsinawa, sai kuma Gidan Sullubawa.

KARANTA: Ba tare da bata lokaci ba: Buhari ya taya Obaseki murnar sake lashe zaben Edo

1. Alhaji Bashir Aminu Bashir Aminu ‘Da ne wajen Sarkin Zazzau Malam Muhammadu Aminu wanda ya yi mulki a baya, bayan rasuwarsa a 1975 ne aka nada Marigayi Shehu Idris, shi ne Iyan Zazzau.

Tsohon Hakimin na Sabon Gari ya fito ne daga gidan Katsinawa wanda Sarki Abdulkarim Mahaifin Sambo ya kafa.

2. Alhaji Mannir Jafaru Mannir Jafaru ‘dan Sarki Jafaru Isiyaku ne wanda ya fito daga gidan Barebari. Yanzu haka shi ne Hakimin Basawa kuma Yariman Zazzau.

Mahaifinsa ya yi mulki zuwa 1955 kafin Sarki Aminu.

3. Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya na cikin gidan Mallawa, yanzu haka shi ne Magajin Garin Zazzau, jika ne na Nuhu Bamalli.

Kamar sauran manyan kasa, shi ma Surukin tsohon Sarki ne.

4. Alhaji Aminu Shehu Idris: Shi ne babban ‘dan Marigayi Shehu Idris, a cikin wannan jeri. Aminu ne ya ke rike da sarautar Turakin Zazzau. Jika ne wurin Malam Idris

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.

Asali: Legit.ng

Online view pixel