Edo: Idan an ga dama za a iya yin zaben kwarai – Fayose ya taya Obaseki, Wike da PDP murna

Edo: Idan an ga dama za a iya yin zaben kwarai – Fayose ya taya Obaseki, Wike da PDP murna

- Ayodele Fayose ya yi magana game da zaben Gwamnan Jihar Edo

- Tsohon Gwamnan ya ce idan an ga dama za a iya yin zaben kwarai

- Dan siyasar ya yi kira ga Godwin Obaseki ya zauna a jam’iyyar PDP

Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Peter Fayose ya na cikin wadanda su ka tofa albarkacinsu game da zaben jihar Edo da aka yi a karshen makon da ya wuce.

Mista Ayodele Peter Fayose ya ke cewa idan an ga dama za a iya yin zaben kwarai a Najeriya,

“Sakamakon zaben jihar ya nuna za mu iya samun zabe na gari, mai kyau da inganci idan masu rike da gwamnatin tarayya sun bada dama ga hukumar INEC da jami’an tsaro su yi aikinsu ba tare da an tsoma masu baki ba.” Inji Fayose.

Fayose ya taya Mai girma gwamna Godwin Obaseki nasarar lashe zaben da zai ba shi damar tazarce, ya ce kalubale ne a kanshi na yi wa talakawansa aiki.

KU KARANTA: Abin da zaben Edo ya ke nufi - Okorocha

Edo: Idan an ga dama za a iya yin zaben kwarai – Fayose ya taya Obaseki, Wike da PDP murna
Fayose ya bukaci Obaseki ya yi wa mutane aiki, zauna a PDP
Asali: UGC

Ya ce da gwamnan, “Mafi muhimmanci kuma ina so in tuna masa cewa jam’iyyar PDP ta cece shi a lokacin da ya shiga wani hali na bukata a tafiyar siyasar.”

‘Dan adawar ya kara da cewa: “Ina taya aboki na, kuma kanina, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas murnar jagorantar jam’iyyar PDP zuwa ga nasara a zaben.”

Tsohon Gwamnan ya kara da addu’ar wannan nasara ta zama silar jam’iyyarsu ta PDP na karbe mulkin kasar nan baki daya daga hannun APC mai mulki tun 2015.

KU KARANTA: Ize Iyamu: Mutumin da ya sha kashi a PDP, ya koma APC, ya sake shan kashi

Mista Fayose ya nuna za a hurowa Obaseki wuta ya sauya-sheka. “Gwamna Obaseki ya cigaba da zama a jam’iyyar PDP, ka da ya damu da matsin-lambar da za ayi masa.”

Ayo Fayose wanda ya sauka daga kan mulkin jihar Ekiti a 2018, bai iya bayyana wadanda za su taso gwamnan na Edo a gaba domin ya tsere daga jam’iyyar PDP ba.

Gajeren jawabin ‘dan siyasar ya kare da cewa: “Ina taya mutanen jihar Edo murna, da kuma ‘yan Najeriya da musamman jam’iyyar PDP na wannan nasara mai dadi.”

Dazu kun samu rahoto game da abin da ake fadawa Adams Oshiomhole da Bola Tinubu a sakamakon gagarumar nasarar da jam'iyyar PDP ta samu a zaben Edo.

Wani bidiyo na Dino Melaye ya na yi wa Oshiomhole da Tinubu shakiyanci ya bayyana a jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng