Kungiyar dattawan Arewa ta nemi a gaggauta korar shugabannin tsaro

Kungiyar dattawan Arewa ta nemi a gaggauta korar shugabannin tsaro

- An sake bukatar Shugaba Buhari da ya sallami shugabannin tsaro

- Dattawan arewa ne suka yi wannan kira biyo bayan ci gaban hare-hare da matsalolin tsaro a fadin kasar

- Hakan ya kasance ne sakamakon lamarin rashin tsaro a Najeriya inda ake samu hauhawan ta’addanci da hare-hare yan bindiga

Kungiyar dattawan arewa maso gabas mai kokarin kawo zaman lafiya da ci gaba, ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi gaggawan sallamar shugabannin tsaro.

A cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun shugabanta, Zanna Goni, kungiyar ta koka kan yadda lamarin tsaro ke kara tabarbarewa a kasar.

Kungiyar ta nuna rashin jin dadi cewa wasu na ganin sun yi shiru ne saboda yankin da shugabannin tsaron suka fito, inda suka ce ko kadan ba haka bane.

A cewar dattawan, sun yi shiru ne tare da fatan cewa abubuwa za su daidaita kamar yadda shugabannin ke yawan fadi, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Kungiyar dattawan Arewa ta nemi a gaggauta korar shugabannin tsaro
Kungiyar dattawan Arewa ta nemi a gaggauta korar shugabannin tsaro Hoto: Femi Adesina
Asali: Twitter

“Amma mun ga cewa duk da kudaden da Shugaban kasarmu ke ba rundunar sojin da kuma tabbacin da shugabannin tsaronmu ke bayarwa na cewa abubuwa za su sauya, babu wasu alamu da ke nuna haka. Wannan abun bakin ciki ne.

“Haka yasa muke jaddada bukatar saka sabbin hannu da za su kawo sabbin manufofi wadanda za su kai ga kawo sauyi a fasalin tsaron kasar.

“Mun ga yadda abubuwa suka dagule a karkashin ikon wadannan shugabannin tsaron.

“Shakka babu yanzu kusan komai ya tabarbare a fadin kasar, yan bindiga na kashe-kashen bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba, yan ta’adda da masu garkuwa da mutane sun zama ruwan dare.

“Wannan abu ya yi sanadiyar jefa jama’a cikin halin fargaba da rashin sanin makama.

“Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saurari koke-koken yan Najeriya ta hanyar sauya fasalin tsaron kasar.

KU KARANTA KUMA: Shugaban APC a Edo ya daura laifin nasarar da Obaseki yayi a PDP kan Oshiomhole

“A matsayinmu na dattawa, ba zai yiwu mu yi gum da bakinmu ba alhali lamarin na damun al’umman kasar.

“Har yanzu mun kasa gane dalilin Shugaban Kasa na ci gaba da aiki da wadannan shugabannnin tsaro duk da kiraye-kirayen da ake masa na sallamar su daga kusan kowane bangare.

“Muna jan hankalin Shugaban kasa kan cewa ’yan kasa sun gaji da tabbacin da ake basu a harkar tsaro amma har yanzu ba sauyi; Suna bukatar gani a kasa,” inji dattawan.

A baya, mun ji cewa kungiyar dattawan arewa ta bayyana dalilinta na tattaunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo tare da kungiyar Afenifere.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya ce sun tattauna da su domin shawo kan matsaloli da manyan kalubale da ke addabar kasar nan, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi ganawar sirri da takwaransa na Ghana a Abuja

An yi taron da Obasanjo, shugabannin kungiyar Afenifere, dattawan arewa, ohaneze Ndigbo da wata kungiyar 'yan yankin Neja Delta, sun yi taron tattaunawa na tsawon kwanaki biyu a Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel