Edo: Mutane sun fito su na yi wa Oshiomhole sheganta saboda nasarar Obaseki

Edo: Mutane sun fito su na yi wa Oshiomhole sheganta saboda nasarar Obaseki

- Mutane barkatai su ka fito su na murnar nasarar PDP a zaben Jihar Edo jiya

- Osagie Ize-Iyamu ya sha kashi a hannun Gwamna mai-ci, Godwin Obaseki

- Wannan rashin nasara za ta taba siyasar Adams Oshiomhole da mutanensa

Sakamakon nasarar Godwin Obaseki a kan Osagie Ize-Iyamu, Jama’a da-dama sun fito su na murna da yadda zaben gwamnan Edo ya kaya a karshen makon nan.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an samu mutanen gari da su ka rika yi wa tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, shakiyanci ganin ‘dan takararsa ya sha kashi.

Fasto Osagie Ize-Iyamu na APC ya zo na biyu a zaben ne da ratar kusan kuri’a 85, 000.

Haka zalika wasu ‘yan siyasa da ke adawa da Adams Oshiomhole sun nuna farin cikinsu a fili da nasarar da gwamna Godwin Obaseki ya samu na zarcewa a kan mulki.

KU KARANTA: Abubuwan da su ka taimakawa PDP wajen doke Jam’iyyar APC a Edo

Daga cikin masu wannan murna akwai Sanata Dino Melaye wanda ya fito a cikin wani bidiyo ya na wake-waken murnar kayin da APC ta sha a hannun jam’iyyaru ta PDP.

Dino Melaye wanda ya bar APC bayan Adams Oshiomhole ya zama shugaban jam’iyya, ya dauki wannan bidiyo ne daga garin Edo, kamar yadda ya bayyana da bakinsa.

Melaye bai tsaya nan kawai ba, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya na cikin na hannun daman Oshiomhole.

Da ya ke magana, Dino Melaye ya ce an kassara Oshiomhole, ya zama yaro a siyasa. “Mutumin da mu ka sani da Osho Baba ya zama Osho Pikin.” Inji tsohon sanatan.

KU KARANTA: Buhari ya taya PDP murnar doke APC a Edo

Edo: Mutane sun fito su na yi wa Oshiomhole sheganta saboda nasarar Obaseki
Wasu na murna da galabar Obaseki kan APC a Edo
Source: UGC

Ya ce: “Ya ka ke tunanin mutumin da ke dauke da lema zai sha kasa a lokacin damina?" Ya kara da cewa: “Motar Dalar kudin da aka kawo jihar Edo ba ta yi aiki ba.”

Obaseki wanda ya bar APC zuwa PDP a watan Yuli ya dauki wani salon yakin neman zabe na Edo no be Lagos domin nuna adawa ga karfin farin jinin Bola Tinubu.

Bayan INEC ta tabbatar da Godwin Obaseki ne ya yi nasara, irinsu Seyi Makinde, Nyesom Wike, Rabiu Kwankwaso da Atiku Abubakar duk sun taya sa murna.

Su kuwa mutanen Twitter cewa su ke yi za a yi gwanjon tsohon shugaban jam'iyyar na APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel