Shugaban APC a Edo ya daura laifin nasarar da Obaseki yayi a PDP kan Oshiomhole

Shugaban APC a Edo ya daura laifin nasarar da Obaseki yayi a PDP kan Oshiomhole

- Shugaban jam’iyyar APC na Edo, Anselm Ojezua ya yi martani a kan nasarar zabe da Gwamna Godwin Obaseki ya samu

- Ojezua ya ce ya samu labarin nasarar Obaseki da wasu yanayi mabanbanta

- Shugaban ya bayyana cewa ya yi bakin ciki da ganin cewa Obaseki bai lashe zaben ba a karkashin APC

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Edo, Anselm Ojezua ya yi bayani kan dalilin da yasa ake ganin laifin Adams Oshiomhole kan kaye da jam’iyyar ta sha a zaben gwamna da aka kammala a jihar.

Ojezua ya yi jawabin yayinda yake martani ga nasarar Godwin Obaseki na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan Edo.

A cewar Daily Trust, Shugaban na APC a Edo, ya ce ya samu labarin nasarar Obaseki a yanayi mabanbanta.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Obaseki ya magantu bayan lallasa Ize-Iyamu na APC da yayi

Shugaban APC a Edo ya daura laifin nasarar da Obaseki yayi a PDP kan Oshiomhole
Shugaban APC a Edo ya daura laifin nasarar da Obaseki yayi a PDP kan Oshiomhole Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya bayyana cewa ya yi bakin ciki da ganin cewa Obaseki bai yi nasara ba a karkashin APC.

Dan siyasan ya yi nuni ga cewa da gwamnan ya lashe zaben a karkashin APC idan da Adams Oshiomhole bai kore shi daga jam’iyyar ba ta hanyar hana shi takara.

Ya ce APC a Edo ta rigada ta goya ma Obaseki baya a matsayin dan takararta kafin aka hana shi takara karkashin jam’iyyar.

“A wannan lokacin na yi furucin cewa babban kadara da muke da ita shine gwamnan. Nasarar da gwamnan ya samu ya gaskata furucin,” in ji Ojezua.

KU KARANTA KUMA: Farin jinin PDP, rikicin APC, gajiya da Oshiomhole, da yadda Obaseki ya zarce a kan kujerar Gwamna

Shugaban ya kuma bayyana cewa shugabannin jam’iyyar na kasa sun karfafa kamfen din Osagie Ize-Iyamu ba tare da jam’iyyar reshen jihar ba.

A gefe guda, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi magana kan rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, biyo bayan kaye da ta sha a zaben gwamnan Edo.

Okorocha, sanata mai wakiltan yankin Imo ta yamma, ya ce APC ta kare, cewa abunda ya rage ma jam’iyyar shine mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ake gani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel