Gwamna El-Rufai ya bada ranakun makoki saboda mutuwar Sarkin Zazzau

Gwamna El-Rufai ya bada ranakun makoki saboda mutuwar Sarkin Zazzau

- Gwamna Nasir El-Rufai ya fitar da ranakun makokin Sarkin Zazzau

- Babu wanda zai fita aiki Ranar Laraba saboda wannan rashi da aka yi

- Alhaji Shehu Idris ya rasu ne a babban asibitin Soji na 44 a Kaduna jiya

Gwamnatin Nasir El-Rufai ta bada ranakun makoki a fadin jihar a sanadiyyar mutuwar Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.

Za ayi kwanaki uku a jere ana makokin Marigayin kamar yadda gwamna ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar 20 watan Satumba.

Al’umma za su yi amfani da wannan dama domin yin addu’o’i da karbar gaisuwar makokin wannan babban rashi da aka yi a jihar Kaduna.

KU KARANTA: Sarkin Zazzau ya rasu

Mai taimakawa gwamnan Kaduna wajen yada labarai, Mista Muyiwa Adekeye, ya ce ba za a rika fito da tutoci sama a wadannan ranaku uku ba.

Gwamna El-Rufai ya bada ranakun makoki saboda mutuwar Sarkin Zazzau
Marigayi Sarkin Zazzau, Shehu Idris
Asali: Facebook

Za a shiga wadannan ranakun makoki ne daga Litinin 21 ga watan Satumba zuwa Laraba, 23 ga wata, inji hadimin mai girma gwamnan Kaduna.

A ranakunan Litinin da kuma Talata za a zo aiki a ofisoshin gwamnati kamar yadda aka saba, amma ranar Laraba babu wanda zai yi aiki a Kaduna.

KU KARANTA: Shehu Idris: An yi rashi - Gumi

A ranar Laraba 23 ga Satumba ne za ayi sadakar uku kamar yadda Musulmai su ke yi. A wannan rana za ayi wa mamacin addu’o’i na musamman.

Shehu Idris ya rasu ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba a asibitin sojoji da ke Kaduna. Gwamna Nasir El-Rufai ya tabbatar da wannan.

Idris shi ne sarkin da ya fi kowa dadewa a tarihin masarautar Zazzau, ya yi shekara 45 a mulki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel