Shehu Idris: Jerin wadanda ake sa ran za su iya rike sarautar kasar Zazzau

Shehu Idris: Jerin wadanda ake sa ran za su iya rike sarautar kasar Zazzau

- A ranar 20 ga watan Satumba ne mutanen Zazzau su ka yi babban rashi

- Mai Martaba Shehu Idris, ya rasu a wani asibitin sojoji da ke garin Kaduna

- Sarkin da ya fi kowa dadewa a mulkin Zazzau ya cika ya na mai shekaru 84

Masana tarihi sun ce Gunguma wani daga cikin jikokin Bayajidda ne ya fara rike sarautar kasar Zazzau. A tarihi an yi sarakunan Habe 60 zuwa Marigayi Shehu Idris.

Legit.ng Hausa ta zakulo jerin wadanda ake tunanin za su iya samun gadon wannan kujera.

Kafin nan ya kamata a san cewa akwai gidajen sarauta daban-dabam a kasar Zariya; Gidan Mallawa, Gidan Barebari, da Gidan Katsinawa, sai kuma Gidan Sullubawa.

Wadanda ke zaben sarki su ne Waziri, Makama Karami, Fagaci da Limamin Kona da na gari.

KU KARANTA: Tarihin Shehu Idris

1. Alhaji Bashir Aminu

Bashir Aminu ‘Da ne wajen Sarkin Zazzau Malam Muhammadu Aminu wanda ya yi mulki a baya, bayan rasuwarsa a 1975 ne aka nada Marigayi Shehu Idris, shi ne Iyan Zazzau. Tsohon Hakimin na Sabon Gari ya fito ne daga gidan Katsinawa wanda Sarki Abdulkarim Mahaifin Sambo ya kafa.

Shehu Idris: Jerin wadanda ake sa ran za su iya rike sarautar kasar Zazzau
Marigayi Sarki Shehu Idris
Source: Facebook

2. Alhaji Mannir Jafaru

Mannir Jafaru ‘dan Sarki Jafaru Isiyaku ne wanda ya fito daga gidan Barebari. Yanzu haka shi ne Hakimin Basawa kuma Yariman Zazzau. Mahaifinsa ya yi mulki zuwa 1955 kafin Sarki Aminu.

KU KARANTA: Sanusi II ya hadu da El-Rufai a Kaduna

3. Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli

Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya na cikin gidan Mallawa, yanzu haka shi ne Magajin Garin Zazzau, jika ne na Nuhu Bamalli. Kamar sauran manyan kasa, shi ma Surukin tsohon Sarki ne.

4. Alhaji Aminu Shehu Idris

Akwai kuma Aminu Shehu Idris, wanda shi ne babban ‘dan Marigayi Shehu Idris, a cikin wannan jeri. Aminu ne ya ke rike da sarautar Turakin Zazzau. Jika ne wurin Malam Idris Auta.

A gidan Katsinawa za a iya samun takara tsakanin babban 'dan Marigayi Shehu Idris, da kuma Iyan Zazzau da Wamban Zazzau, Alhaji Abdulkareem Aminu, Hakimin Giwa.

Daily Trust ta ce daga gidan bare-bari, Yariman Zazzau ba zai fuskanci takara sosai ba.

A bangaren gidan Mallawa bayanAhmad Bamalli akwai manyan sarakai irinsu Ciroman Zazzau, Alhaji Sa’idu Mailafiya da Barden Kudun Zazzau, Alhaji Hassan Tijjani.

Gidan karshe a kasar Zazzau shi ne na Sullubawa inda a halin yanzu babba a gidan ya tsufa tukuf. Dan Galadiman Waziri ya na cikin wadanda za su iya neman sarauta daga nan.

A jiya kun ji cewa Gwamna Nasir El-Rufai ne ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya kuma sanar da lokacin da za ayi jana'izar Mai martaba bayan ya cika a safiyar Ranar Lahadin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel