Hankalinmu ba zai kwanta ba har sai an fadi sakamakon zaben kananan hukumomi 2 - PDP
- Jam’iyyar PDP ta nuna bacin ranta a kan jinkirin da hukumar INEC ta yi wajen sanar da sakamakon sauran kananan hukumomi biyu a zaben gwamnan Edo
- PDP ta bayyana cewa ba za ta lamunci kaddamar da zaben a matsayin ba kammalalle ba
- Zuwa yanzu dai Obaseki na gaba da dan takarar APC, Osagie Ize-Iyamu
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi korafi a kan tsaikon da aka samu wajen sanar da sakamakon kananan hukumomi biyu da suka rage a zaben gwamnan jihar Edo.
Babbar jam’iyyar adawa ta kasar ta ce lallai an kammala zaben gwamnan Edo.
PDP ta jaddada cewa ba za ta lamunta ba idan har hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi yinkurin bayyana zaben a matsayin ba kammalalle ba.
KU KARANTA KUMA: Sakamakon zaben Ƙananan hukumomi 16: Obaseki ya zarce Ize-Iyamu da ƙuri'u 87,677
Ta sanar da hakan ne a wata wallafa da tayi shafinta na Twitter, inda tace: “#EdoDecides2020: Jan hankali – Jinkirin da @inecnigeria wajen sanar da sakamakon kananan hukumomi biyu da suka rage baa bun yarda bane. An kammala zaben gwamnan Edo. Don haka muna watsi da duk wani yunkuri na kaddamar da zaben a matsayin ba kammalalle ba."
A gefe guda, mun ji cewa jami'in da ke tattara zaben karamar hukumar Orhionmwon, jihar Edo ya yi batan dabo.
Kamar yadda BBC ta ruwaito, hukumar INEC ce ta fara bayyana fargabarta na rashin sanin inda jami'in nata ya ke, a lokacin da ake tattara sakamakon zaben gwamnan jihar.
Da farko, wani jami'in PDP ne ya hankaltar da mutane kan batan jami'in, sai dai wani jami'in APC ya karyata zarginsa, yana mai cewa PDP na son ta yi magudin zabe ne kawai.
KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: An harbi ma'aikacin INEC, an raunata wani ma'aikacin wucin gadi
Kamar yadda BBC ta ruwaito, an tabbatar da ganin jami'in hukumar ta INEC a cibiyar tattara sakamakon zaben, sai dai, an neme sa an rasa daga baya.
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC a cewar jaridar Sahara Reporters, ta tabbatar da batan jami'in nata, tana mai cewa jami'in ya bata ne jim kadan bayan zuwansa cibiyar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng