Sakamakon zaben Ƙananan hukumomi 16: Obaseki ya zarce Ize-Iyamu da ƙuri'u 87,677
- Hukumar zabe ta saki sakamakon zaben kananan hukumomi 16 a jihar Edo
- Dan takarar jam’iyyar PDP, Godwin Obaseki ne kan gaba zuwa yanzu
- Akwai takarar kuri’u 87,677 tsakaninsa da dan takarar APC, Osagie Ize-Iyamu
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na ci gaba da sakin sakamakon zaben gwamnan jihar Edo wanda aka gudanar a ranar Asabar, 19 ga watan Satumba.
Zuwa yanzu dai dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Godwin Obaseki ne kan gaba. Akwai tazarar kuri’u kimanin guda 87,677 tsakaninsa da dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Osagie Ize-Iyamu, wanda shine ke biye da shi.
Sahara Reporters ta ruwaito cewa bayan sanar da sakamakon kananan hukumomi 16, Obaseki ne a kan gaba. Saura kananan hukumomi biyu a nan gaba.
KU KARANTA KUMA: Jan hankali: Muhimman abubuwa 5 da suka faru a ranar da aka gudanar da zaben Edo
Ga jerin wadanda aka sanar zuwa yanzu:
1. Karamar hukumar Igueben
APC: 5,189
PDP: 7,870
2. Karamar hukumar Esan ta Arewa maso gabas
APC 6559
PDP 13,579
3. Karamar hukumar Esan ta tsakiya
PDP: 10,694
APC: 6,719
4. Karamar hukumar Ikpoba Okha
PDP: 41, 030
APC: 18, 218
5. Karamar hukuma Owan ta gabas
APC: 19,295
PDP: 14,7626.
6. Karamar hukumar Estaka West
APC: 26,140
PDP: 17,959
7. Karamar hukumar Egor
APC: 10, 202
PDP: 27, 621
8. Karamar hukumar Esan ta yamma
APC - 7,189
PDP - 17,433
9. Karamar hukumar Uhunmwonde
PDP: 10,022
APC: 5,972
10. Karamar hukumar Ovia ta Arewa
APC - 9907
PDP - 16, 987
11. Karamar hukumar Esan south East
APC: 9,237
PDP: 10,563
12. Karamar hukumarsa Oredo
APC: 18,365
PDP: 43,498
13. Karamar hukumar Owan West
APC - 11,193
PDP - 11,485
14. Karamar hukumar Etsako Central
APC - 8359
PDP - 7478
15. Karamar hukumar Akoko Edo
APC - 22,963
PDP - 20,101
16. Karamar hukumar Etsako East
APC - 17, 011
PDP - 10,668
KU KARANTA KUMA: Sakamakon zaben gwamnan jihar Edo: APC na shan kaye
A halin da ake ciki, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da matsa wa hukumar zabe mai zaman kanta canja sakamakon zaben gwamna a sassa daban-daban na jihar Edo.
A cikin wata sanarwa a ranar Asabar, Kola Ologbondiyan, babban sakataren jam’iyyar na kasa, ya bukaci Mahmood Yakubu, Shugaban INEC, da kada ya amsa kiran domin hadin kai da zaman lafiyan kasar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng