Bidiyo: Rundunar soji ta kama dilan makaman 'yan bindigar Zamfara

Bidiyo: Rundunar soji ta kama dilan makaman 'yan bindigar Zamfara

- Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa ta kama wani mutum mai suna Usman Ibrahim da tarin alburusai da karamar bindiga da kuma kudi

- A cewar hedikwatar rundunar tsaro, binciken farko-farko ya nuna cewa Ibrahim dilan makamai ne da ke safararsu zuwa arewa maso yamma

- Kazalika, an kama wasu mutane biyu; mace da namiji, da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi domin sayarwa 'yan bindiga a Zamfara

Dakarun rundunar soji na cigaba da samun nasara a yakin da su ke yi da aiyukan ta'addanci a yankin arewa maso yamma.

A cikin wata sanarwa da hedikwatar rundunar tsaro ta fitar ranar Juma'a, ta bayyana cewa dakarun soji a karkashin atisayen HADARIN DAJI sun samu nasarar cafke wani babban mai laifi.

Manjo Janar John Enenche, shugaban sashen yada labarai a hedikwatar tsaro ta kasa, ya ce wasu sojoji sun kama wani mutum mai suna, Usman Ibrahim, wanda ake zargi da safarar makamai.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta tura jami'an da za su share cibiyoyin kada kuri'a da tattara sakamako

An kama Ibrahim da carbi 890 na wasu alburusai na musamman da ya boye a abin hawansa, kamar yadda Enenche ya bayyana wa manema labarai.

A cewar Enenche, jami'an rundunar atisayen SAHEL SANITY ne suka kama Ibrahim bayan samun muhimman bayanan sirri daga dakarun rundunar atisayen HADARIN DAJI.

Bidiyo: Rundunar soji ta kama dilan makaman 'yan bindigar Zamfara
Manjo Janar Enenche
Asali: UGC

Rundunar soji ta bayyana cewa ana zargin Ibrahim, dan asalin garin Riyom a karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato, da safarar makamai zuwa yankin arewa maso yamma.

Kalli faifan bidiyon jawabin Janar Enenche:

Bayan tarin alburusan, an samu wata karamar bindiga a wurinsa da katin shaidar aikin dan sanda da kuma kudi N2,230,000.

Enenche ya bayyana cewa binciken farko-farko ya nuna cewa Ibrahim babban dila ne dake sayowa 'yan bindiga makamai.

DUBA WANNAN: Sunayensu: Hameed Ali ya nada DCGs 2, ACGs 5, ya sauya wa manyan jami'ai 5 wurin aiki

Kazalika ya bayyana cewa an kama wasu mutane biyu da ake zargin suna sayowa 'yan bindiga miyagun kwayoyi.

Mutanen biyu; Kabiru Dauda da Hafsat Musa, sun shiga hannun jami'an tsaro a Gusau yayin da ake binciken ababen hawa.

An kamasu da wasu kullin ledoji da ke dauke da ganyar tabar wiwi da sauran miyagun kwayoyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel